Addini

Abinda ke cikin Tiktok fito-na-fito da Allah da tallata aikin Shaidan – Dr Mansur Sokoto

Advertisment
Abinda ke cikin Tiktok fito-na-fito da Allah da tallata aikin Shaidan - Prof Mansur Sokoto
Prof Mansur Ibrahim sokoto

Jiya wasu yan uwa masu kishin watsa addini suka ba da shawarar mu shigar da karatukanmu a waccan manhajar da na ambata a sama.
Kasancewar na san #Socialmedia takobi ne mai kaifi biyu ban yi wata wata ba na karbi shawarar da hannuwa biyu.

Bayan da na sauke manhajar na yi minti 30 a ciki sai nan take tunanina a kan lamarin ya canja. Lallai kamar yadda Bahaushe yake cewa ne, *Gani ya Kori Ji*; abinda na gane ma idona bai yi mani dadi ba ko kadan. Babu shakka makiyanmu sun samu galaba a kan mu.

Iyakar abinda na gani na wa’azi a manhajar shi ne irin abinda yan sharholiya za su yanko daga cikin tuntuben harshen malami ko wani yanki na raha da sakin jiki. Amma ilahirin abinda ke ciki fitsara ce da yin fito-na-fito da Allah da tallata aikin Shaidan.

Bisa ga haka, a sabuwar fahimtata wannan Tik tok yakar sa ya kamata ayi a raba yayanmu da shi – maza da mata – maimakon kokarin kyautata shi. Bahaushe ya ce A dauri kashi ko a bata igiya?
Zan yi amfani da wannan dama in shawarci iyaye da mazaje masu iyali su kula sosai kuma su sa ido bisa amanar da Allah ya ba su kan manhajojin da iyalansu suke ta’amuli da su. Ko babu komai “Lokaci shi ne rayuwa”. Ina amfanin mutum ya kashe rayuwarsa ga abinda babu alherin duniya bale na lahira a cikin sa.
Ya Allah, na yi nawa wanda nike iyawa, shi ne fadakarwa. Allah ka shaida, kuma Allah ka shigar da shiriya ga yayan Musulmi da iyalansu
✍️ Mansur Sokoto
Jum’ah 2 Rajab 1443H (04/02/2022)

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button