Addini
Masha Allah ! Dakta Gumi ya fara shiga rugga da kauyaku a daji yana koya masu addini da da’awah (Hotuna)
Advertisment
Shaikh Dakta Ahmed Gumi ya fara ziyartar rugar Fulani da kauyaku domin yi masu da’awah da karantar dasu addini.
Shehin Malamin a yau Asabar ya kewaya kauyaku da ruga a garin Jere inda ya debi litattafai da sauran kayan karantarwar Addini da zai taimakawa mazauna kauyakun su fahimcin karantarwar addinin musulunci a saukake.
Manuniya ta ruwaito Daktan yayi imani cewa ta hanyar karantar da Fulani da kauyawan ne kadai za a samu raguwar hare-haren ta’addanci da garkuwa da mutane dake faruwa a kasarnan.
A da’awar tashi ta yau Shehin Malamin ya yiwa kauyawa da Fulanin bayani akan su san Allah da tauhidi da musulunci da sai sauransu.