Dr. Sheikh Mansur Yelwa yayi Martani akan Fim din hausa da ake koyar da Jima’i
Fim mai suna Makaranta (the school) wanda anka fara tallar shi a yan kwana kinki nan wanda zakuji irin yadda ake koyar da Jima’i ga yan mata da maza a a cikin aji wanda sunka sanya masa suna “Makaranta”.
Wanda shine mutane sunka fara nuna rashin jindadi a kasar hausa wannan abu na faruwa inda tashar arewa24tv ta sanya.
Shine fitaccen marubucin nan Datti asslafy yayi magana da cewa
“MANUFAR AREWA 24 YA FARA BAYYANA
Sun fara tallen wani fitsaararren film wanda yake koyar da zallan ziina da lalaata da maadigo, da yadda budurwa maziinaciya zata kare kanta daga samun cikin sheege ko da tana gaban iyayenta, sunan film din Makaranta
Mun fada kuma zamu cigaba da fada, ku neesanta gidajenku da kallon Arewa 24 da duk wata kafa dake da alaka da su, imba haka ba da wahala kuyi alfahari da ‘ya’yanku ranar Hisabi
Yaa Allah Ka amintar da mu daga al’amuran Yehudawan duniya”
Shine dr mansur isah yelwa ya nuna goyon bayansa akan maganar datti asslafy.
“Wannan gaskiya ne. Ina tare da kai anan. Allah Ya yi maka albarka.
Allah Ka sa mutane suyi aiki da wannan nasiha.”
Ga tallar fim din Nan
Video tallan fim din hausa da ake koyar da Jima’i/saduwa
WANNAN ZAMANI SAI DAI INNALILLAHI WA’INNA RAJI’UN
Saboda Arewa 24 Bata Musulmai bace kocan Asalin Yanda take Gudqnqr dq Ayyukanta Kai Kasan Cewa Tayahudawace Da Masu taimakamasu
Sukuma hukumominmu Babu Wata doka dazasu Qirqiro da xatataimakama Addinin Musulunci
AMMAN DA Abinda yashafi Mulkinsune Dayanxu Wanda zasuje Gidan Yari Harsunkama Hanya
Ya Allah kakiyayemana Qasar Hausa Da Addininmu !!!
Wannan aikin ba mallamai kadai za’a bari dashi ba, yafi karfin su. Wannan aikin hukumomin jihohin Arewa ne musamman wayanda suka ce sun Shar’ah. Wallahi Allah sai Ya tambayi duk wani gwamna da ya bari ana yada irin wannan fadadi a jihar sa. Haka ma Buhar, ya iya dakatar da twitter saboda ta bata mashi rai amma sabon Allah da lalata tarbiyyar yayan mu bai isa ya bata mashi ran da zai dakatar da AREWA 24 ba