Kannywood

Au’uzubillahi : Addu’ar muce ke bin Maryam Yahaya

Advertisment

Maryam YahayaWata budurwa mai amfani da suna Fatimaumsiun a shafinta na TikTok ta wallafa wani bidiyo wanda wani ma’aboci amfani da Facebook, Sada bn Suleiman Usman ya kwafo ya wallafa a shafinsa ta ce kanwar wannan saurayin da a bara ya wanko kafa tun daga jihar Yobe har Kano don ganin jaruma Maryam Yahaya.
Budurwar wacce ta ke magana cike da takaici inda har sautin kukanta aka dinga ji yana fita ta ce alhakinsu ne ya kama jarumar har ta fadi mummunan ciwon da ta rame kuma halittarta ta sauya.
Kanwar Saurayin da ya sha fiya-fiya saboda Maryam Yahaya ta ce alhakinsu ne ya kama jarumar
Idan ba a manta ba, jarumar ta fadi ciwo wanda har yanzu ba ta dawo yadda take ba inda aka ga ta rame, rama mafi muni wanda har wasu su ke yi mata izgili idan ta wallafa hotunanta a kafar sada zumunta.
Sai dai a bangaren budurwar, ta ce ta yuwu addu’arsu ce ta kama jarumar don ta nuna musu rashin imani.
 
Kamar yadda Fatima ta ce, yayanta ne saurayin da ya je Kano daga Yobe ba tare da sanin kowa ba, ya tsallake ‘yan mata da dama sannan ya isa wurinta, amma ta yi kunnen uwar shegu ta ki sauraronsa.
Cikin fushi ya dauki fiya-fiya yasha, har a haka jaruma Maryam Yahaya bata kalle shi ta tausaya masa ba duk da har asibiti aka kwantar da shi.
Ta kara da cewa yanzu haka kaf mutanen gidansu sun tsani jarumar kuma sun dinga yi mata addu’o’i marasa kyau, kuma alamu na nuna cewa alhakinsu ne ya kama ta.
A cikin bidiyon da ta wallafa a shafinta na TikTok, ta karasa shi tana kuka don idan mutum ya saurara zai ji shasshekar kuka yayin da ta ke kammala bidiyon.
Mu na yi wa jarumar fatan samun lafiya tare da shawartar jarumai akan gudun wulakanta masoyansu, don ba su san inda rana zata fadi ba.
Zaku iya sauraren kanwar matashin a nan.
https://youtu.be/6gxyLgLOdmE

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button