Kannywood

Duk namijin da ya ke barin matarsa ta na rawar TikTok ba zai ji kamshin Aljannah ba – Rukayya Dawayya

Duk namijin da ya ke barin matarsa ta na rawar TikTok ba zai ji kamshin Aljannah ba - Rukayya Dawayya
Rukayya Dawayya

Jaruma Rukayya Dawayya a wani bidiyo da ta yi wanda Hadiza Gabon ta wallafa a shafinta na Facebook ta ja hankali ga mata musamman masu aure da su ke raye-raye a shafukansu na TikTok.
Jarumar ta fara ne da bayar da wani labari takaitacce wanda ta ce ya auku da ita a lokacin tana da aure.
Jarumar ta fara da bayyana yadda wasu shakikan kawayenta su ka kai mata ziyara gidanta da ke Abuja bayan ta ci kwalliya amma mijinta bai gani ba.
Tun samun labarin sun kai mata ziyarar our ta nuna a sanar dasu cewa bata nan duk don kada su ga kwalliyarta kafin mijinta.
A cewar jarumar, har sai da mijinta ya dawo ya ga kwalliyar sannan daga bisani ta kira su ta ce musu ta dawo daga inda ta je.
Daga karshen bidiyon ta ce duk macen da ke yin kwalliya ta wallafa bidiyon kwalliyar a TikTok bata son mijinta, yayin da mazan da su ke barin matansu su na bidiyon ba sa kaunar matan kuma basa kishinsu.
Jarumar ta ce ko kamshin Aljannah namiji mara kishi ba zai ji ba, saboda hakan fadin manzon Allah (SAW) ne.
Ta ce da ace mata za su ga wasu mazan da ke kallon bidiyonsu na TikTok da ba su yi ba tun farko da har kuka sai sun yi.
A cewar jarumar, “Duk macen da ta ke son mijinta tana killace kanta ne tare da boye surar jikinta, mijinta kadai za ta bayyana wa su.”
Jarumar ta kara da cewa duk namijin da ya ga bidiyon matar aure a TikTok ba zai so ya kara gani ba saboda shi ma ba zai so ta shi ta yi bidiyo irin wannan ba.
Daga karshe jarumar ta yi addu’a inda ta ce Allah ya yi mana maganin bala’in da ya shigo, wai shi TikTok.
Da fatan masu yi za su kiyaye kuma su ji wa’azin nata da kunnen basira.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button