Kannywood

Martanin Darakta Falalu Dorayi Ga Shuwagabanni akan kashe Mutanen Goronyo A Sokoto

Falalu Dorayi Yayi Alhini Da Kalamai Masu Hikima Cikin Bacin Rai Akan Kashe Mutane A Sokoto

Advertisment

Martanin Darakta Falalu Dorayi Ga Shuwagabanni akan kashe Mutanen Goronyo A SokotoA shekaranjiya ne ranar lahadi misalin karfe 4 da wani abu na yamma Yan fashin daji wato yan bindiga sunka kai mumumman hari a kasuwar goronyo da ke jahar sakkwato inda sunka kashe mutane da dama sunka raunata wasu.
Inda kuma sunka yi asarar dukiyoyin mutane sosai a ciki shine wannan fitacen marubuci kuma darakta a masana’antar kannywood yayi martani ga shuwagabani akan irin yadda halin da talakawa suke ciki a shafinsa na sada zumunta ga abinda yake cewa.
SOKOTO Goronyo Market
Kalmomi Guda 2
HAKKI DA AMANA
suna da nauyin da kowa sai an masa tambaya akansu. Tsakanin mutum da iyalinsa, ‘Yan uwansa, Makotansa, Abokansa.
Sai babban nauyi mafi girman bala’i wato MULKI, ko Yaushe masu milki zasu farka su yi tunanin tarin tuhumar rayuka da dukiyar Al’ummar da suka salwanta saboda sakaci da son zuciyarsu, tuhuma ce da take jiran duk mai MULKI tun daga zamansa a KABARI har zuwa filin ALKIYAMA.
Akwai mamaki da takaici, duk da ance an zuba matakan tsaro a SOKOTO da ZAMFARA Amma a shiga Kasuwar Garanyo a kashe RAI sama da 50, a kore shanu da tumaki a KONE gurin Sana’a da ababan hawan al’umma.
Kuma duk lokacin da aka dauka ana yi Gwamnati da Jami’anta basu zo ba.
TO AI SHIKENAN.
Idan bukatar kansu ce sukan tara Jami’an tsaro da bindugu kai kace yakin duniya na 3 za’a yi. Mun gani kwanannan a zaben Local government da zaben Shugaban Jam’iya. Amma ana kashe Yara, Mata, tsofaffi, Magidanta, ai wa mata fyade a kone gidaje da dukiyoyi. Ina alkawarin da kuka dauka?
Muna rokon Allah Jallah Wa Alah, Yadda akai addu’a ruwan sama ya dawo, Allah ka Kawo mana karshen wannan rashin imani.
Duk wanda yake da hannu a cikin ko ya sani ya ki magana, Allah ka tona asirinsu. Amin. Ya Hayyu Ya Qayyum.
#falaluadorayi”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button