Sai An Biya Ni Diyyar Naira Milyan Dari Kan Amfani Da Wakata Da Aka Yi Ba Da Izinina Ba, Inji Nazir M. Ahmad
Shahararren mamawakin Hausan nan Naziru M. Ahmad wanda aka fi sani Da Sarkin Waka ya nemi diyyar naira milyan dari daga wajen Ebonylife T.V.sakamakon yin amfani da wakar sa da suka yi a fim din su ba tare da izininsa ba.
Ga cikkakiyar hirarsa da Usman Mu’azu kan lamarin.
Da farko zamuso ka gabatar da sunanka?
Sunana Naziru M. Ahmad (Sarkin Waka).
Mun samu labari akwai wani gidan talabijin da yake amfani da wata waka taka ko za ka fada mana wace waka ce?
Eh, sunan wakar bincike, muna ce mata bincike.
Mun samu labarin suna amfani da wannan wakar bada izininka ba haka ne ko yaya abin yake?
Hakane suna amfani da ita bada izinina ba kuma mun nemi su fada mana dalili sun yi shiru, shine muka ce za mu bi hanyar da ta dace domin karbar hakkinmu.
Ta wace hanya kuka yi kokarin sanar da su?
Mun bi ta hanyar lauyan mu domin ya tura musu a rubuce, kuma ya yi hakan amma ba su ce komai ba.
To amma bayan wannan matakin wane irin mataki nan gaba kuke ganin za ku dauka?
Eh, mataki na gaba shine za mu sake tura musu kamar yadda muka yi a baya, amma idan ba su ce komai ba zamu bi wata hanyar da ta dace ta kotu domin idan suna ganin sun fi karfin mu to ba su fi karfin doka ba.
Malam Nazir mai karatu zai so ya ji wai shin ta ina suke amfani da wannan wakar taka?
Suna amfani da ita ne ta hanyar sa ta a cikin wani ‘Series’ dinsu mai suna ‘SON OF THE CALIPHATE’ Season 1.
Sun sa ta ne a matsayin kidan taushi na fim din wato ‘sound track’, saboda sun raina mu, shine muke ganin bai kamata su ci bulus ba, idan sun saba yi wa wasu haka su share to mu ba za mu bari ba.
Idan na fahimce ka wannan dalilin ne ya sa kake neman hakinka a gunsu?
E wannan shine dalili, saboda su yi min bayani wa ya ba su kaya na ba da izini na ba.
To kai yanzu kana da hujjojin da za su tabbatar da wannan abin da kake zargi?
Kwarai kuwa.
Kamar me dame ka tanada da za ka gabatarwa kotu idan ta bukaci hakan?
Akwai hotuna da datas na mintuna da lambar season din da lambar ‘episode’ din da aka yi amfani da kayan nawa.
Dama a doka idan aka yi amfani da kayanku irin haka wace hanya ake bi dan ganin an warware matsalar, ta yaya za’a warware matsalar?
Diyya za su biyani na amfani da kayana ba tare da na sani ba, tun da doka ta ba ni dama na yi hakan.
Akwai abinda ka kiyasta za su baka ne?
E munyi magana da lauyoyi na sun ce a yi musu saukin rangwame su biya naira miliyan dari kawai, saboda a gargade su dan gaba kar su kara taba min kayana.
Ba za ka yi musu sauki ba saboda ganin cewa kamar kudin sun musu yawa?
Kai ne suka yi wa yawa, ni a guri na ma ban samu yadda nake so ba, na yi musu haka ne saboda shine na farko da suka yi min, kuma tunda ka ga sun dauka abin ne ya yi musu kyau tunda ba za su dauki abinda zai lalata musu aiki ba, to sun yadda na sha wahala wajen yin wakar ne shi ya sa bai kamata ya yi kasa da haka ba.
Baka ganin cewa sakaci da kuke nunawa game da kayanku ne ya bada dama suka yi muku wannan abin?
A’a ni ba na sakaci da kayana tunda duk abinda nake yi da ya shafi fasaha ta ina masa copy right ka ga ba za ka ce na yi sakaci ba.
Yanzu ka kai kara kotu ne ko dai za ka kai nan gaba?
Ai tuni maganar tana kotu, muna jiran lokaci ne kawai.
A karshe wani irin kira ko shawara za ka baiwa abokan sana’arka game da irin wadannan matsalolin?
Shawarar da zan ba su ita ce su dinga kula da duk abinda ya shafe su suke da hakkin mallakar sa, domin kare mutuncin hakkin kayansu.
Mun gode.
Nima nagode.