Hukuncin Wanda Yayi Zina Da Matar Da Zai Aura


Assalamu Alaikum malam barka da warhakah. Tambaya daga Dalibinka daga danko wasagu L. G na kasance ina da wacce za muyi Aure da ita amma na biya sadaki saidai muna saduwa da junanmu amma ban bari maniyina ya Zuba daga naga zaizo sai in cire, bana bari ya Zuba kuma Nagaji dayin haka gashi Aure ya kusa menene hukuncina?
AMSA.
Hukuncinka daidai kake da kowanne mazinaci. Sai dai kai naka laifin yafi muni tunda aciki har dacin Amana wato zamba cikin Aminci.
Iyayenta sun Amince dakai, sun yarda zasu baka Aurenta har an dauki rana, amma ka biyewa shaidan ka yaudari ‘yar mutane kana zina da ita.Zina dabi’a ce ta marassa cikakken Imani. Manzon Allah (Saw) yace “Mazinaci ba Zaiyi zina Alhali yana mumini ba”.
Rashin zuba maniyyinka acikin mahaifarta bazai sa kasamu wani sassauci acikin Girman laifin ba. Don haka nake jan hankalinka cewa kaji tsoron Allah ka tuba ka Daina wannan Zinar da kukeyi. Amma ka sani cewa wajibi ne tayi istibra’i kafin a Daura muku Aure. (wato Zata zauna A gida har sai tayi jini uku). Amma wasu Malaman sun ce koda jini guda ne ya wadatar.
GARGADI :
Anan nake jan hankalin iyaye cewa kada ku rika barin ‘yarku tana kebancewa da saurayi koda bayan ya biya sadakin nata ne. Kada ku Amince da irin wannan barnar.
Biyan sadaki ‘daya ne kawai daga cikin sharudan Aure amma ba shine Auren ba. Don ya biya sadakinta bata zama matarsa ba. Ko mutuwa yayi babu gado a tsakaninsu.
Don haka idan zaizo hira ya rika zuwa da yamma, ido na ganin ido. Kuma ku samo wata Qanwarta mai wayo ku zaunar da ita tare dasu.
Mutukar Baligi ya kebance da baliga to Shaidan fa shine na ukunsu. Zai rika cusa musu sha’awar junansu har sai sun fara taba jikin juna, daga nan kuma sai zina.
Allah shi kiyayemu ya kiyaye mana zuriyarmu.
DAGA Zauren fiqhus Sunnah
One Comment