Zango Ya Fito Daga Korama Ya Shigo Teku – Ganduje
“Da wannan babban kifi yana cikin korama amma yanzu wannan babban kifi ya shigo cikin teku.” Ganduje ya ce a lokacin da Zango ya kai masa ziyara.
Fitaccen Jarumi kuma mawaki a masana’antar Kannywood, Adam A. Zango ya gana da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.kamar yadda jaridar voahausa na ruwaito.
Ganawar na zuwa ne bayan da Zango ya sake komawa jam’iyyar APC a kwanan nan.
A shekarar 2019 Zango ya koma jam’iyyar PDP, inda ya nuna goyon bayansa ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar gabanin zabe.
Sai dai kusan makonni biyu, jarumin na Gwaska ya koma gidan da ya fito.
“Da wannan babban kifi yana cikin korama amma yanzu wannan babban kifi ya shigo cikin teku.” Ganduje ya ce a lokacin da Zango ya kai masa ziyarar.
“Yanzu zai yi ta walwala ba tare da ya bugi bango jikinsa ya kuje ba.”