Labarai

labarin Mai Dadi Daga Garin Baga A Borno: Bayan Shekaru 10 Da Barin Garin,Yau Sun Dawo Gida

Advertisment

A karon farko, tun bayan kusan shekaru 10 da mutane suka bar garin Baga garin kasuwanci da safaran kifi, saboda ta’addancin Boko Haram, ina mai shaidawa duniya cewa da yammacin yau lahadi 13-9-2020 tawagar ma’aikata wadanda zasu tsaftace garin Baga sun isa garin kafin isowar mu isowar dubbanin mutanen garin.
Wannan hoto da kuke gani shine tawagar farko na ma’aikata da wasu mutane kusan mutum dari biyu tare da motoci 22 dauke da kayan aiki a lokacin isowarsu garin Baga daga Maiduguri, zasu tsaftace garin Baga
Daga cikin abinda zasu farayi gobe a garin Baga shine share gurare masu muhimmanci da gidajen mutane, da kafa dakunan agajin gaggawa da asibiti da gyara kayayyakin sadarwa, da gyaran rijiyoyi da burtsatse da sauransu.
Datti Assalafy ya cigaba da cewa sai kuma wani abu wanda bai kamata na bayyana ba saboda yanayi na tsaro, sai gobe idan Allah Ya kaimu
Garin Baga ta dawo da taimakon Allah, Jama’a kuyi jinjina ga Maigirma gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum da kuma Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya, tabbas gobe da labari, zaku ga hotuna Insha Allah
Gwamna Zulum jarumi ne, hakika yayi gaskiya da yace idan har bamu cire tsoro ba to yakin nan ba zai kare ba
Yaa Allah Ka nuna mana karshen ta’addancin Boko Haram, Ka tona asirin wadanda suke cin amanar tsaron Nigeria Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button