Musulunci Muke yi Ba Maguzanci ba – Datti Assalafy
بسم الله الرحمن الرحيم
Wannan sakon ya shafi Gwamnatin Khadimul Islam Dr Abdullahi Umar Ganduje, da hukumar Hisbah na jihar Kano, da ‘Yan Sanda, da NDLEA reshen jihar Kano da kuma kungiyoyin kare hakkin yara mata Datti Assalafy ne ya ruwaito
Akwai wani yaro matashi ban san asalin sunansa ba, amma ana masa lakabi da Mista 442, matashi ne da ya zama anno ba a cikin al’ummar Musulmi
Mista 442 yayi garkuwa da wata yarinya da ta shahara da sunan Safara’u, ya dauketa daga gaban iyayenta ya mayar da ita kwana a hotel, yana bata miyagun kwayoyi masu bugarwa, ya lalata mata rayuwa, sannan yana yin wakokin batsa da ita suna fesawa a tsakanin al’ummah
Abi mafi ban tsoro shine, wakokin iskanci da batsa da suke yi yana matukar tasiri, domin duk inda kazo wucewa zakaji yara kanana suna rera wakokinsu na batsa, to wannan babban barazana ne ga lalacewar al’ummah sanadiyyar wannan mu gun halitta 442
Na tabbata wannan wakilin ib_lis bai fi karfin doka ba, Gwamnatin Kano zata iya daukar mataki kansa saboda ta kare al’ummah daga lalacewa, hukumar ‘yan sanda zata iya daukar mataki kansa saboda yayi garkuwa da ‘yar mutane, hukumar Hisbah zata iya shiga don yana kwana da ‘yar mutane a hotel, hukumar NDLEA zata iya daukar mataki kansa domin suna tu’ammali da miyagun kwayoyi sosai, a gwada jininsu za’a tabbatar da kwayoyin da suke sha
Muna kira da babban murya, wannan shai.. danin yaro yana cutar da mu, a dauki matakin doka na gaggawa a kansa
Muna fatan Allah Ya isar da sakon inda ya dace, Ya bada ikon daukar mataki Amin