Uncategorized
Annabi Muhammad Shine Wanda Ya Fi Kowane Mutum Nagarta- Jaruma Rani Murkeji
Advertisment
A yayin da wasu jahillan masu zane-zane, ‘yan fim da marubuta a Indiya ke walakanta Manzon Rahama ta hanyar aikinsu, wata shahararriyar ‘yar Indiya din Rani Mikerji a shafinta na Twitter, ita ikirari ta yi cewa har yanzun a mutum ba a yi kamarSa ba.
Rani Mukerji ta ce, Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare Shi mutum ne mai inganci wanda a tarihin dan Adam har yanzun babu kamarSa.
“Na karanta rayuwarsa da halayen Annabi Muhammad sai na gane cewa Ya fi kowa nagarta.”
Rani Murkeji wacce addininta Hindu ne, shahararriyar ‘yar fim Indiya ce da ta lashe kyaututtuka da dama don kwarewarta a harkar fim.
Advertisment
Madogara: facebook/Dokin Karfe
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com