Uncategorized

Ma’aurata zallah: Yin Jima’i Sau 21 A Wata Na Kare Namiji Daga Kamuwa Da Cutar Daji

Wata likita wadda take hada maganin gargajiya Dokta Ebenezar ta yi kira ga maza da su rika saduwa da matan su akalla sau 21 a  ko wanne wata ko kuma sau biyar a ko wanne mako.

Likitar ta bayyana cewar yin haka na bayar da wata kariya ne ga maza daga kamuwa da cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina.

Ebenezar da ke aiki da asibitin gargajiya mai suna ‘Amuzu Hospital’ a jihar Imo ta ce ta yi wannan kira ne bisa ga sakamakon binciken da likitoci daga jami’ar ‘Habard’ dake kasar Amurka suka yi kuma aka wallafa a wata  jaridar kasar.

Bisa ga rahoton binciken da suka yi akan maza 32,000 ya nuna cewar mazan dake yawan saduwa da matan su basu kamuwa da cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina.

Wani jami’in kungiyar likitocin na kasar Amurka Dokta James Balch ya tabbatar da hakan, inda kuma ya kara da cewa namiji zai iya samun wannan kariya ne idan ya hada da jima’i da cin abincin da zai kara masa karfin garkuwar jikin sa.

Rahotanni sun nuna cewar cin ‘ya’yan itatuwa, ganyen da ake ci, dabino, madara,aya, namijin goro da dai sauran su na kara wa maza kuzari.

Idan ba mantawa aka yi ba  acikin watan Fabrairun  na shekarar 2019 ne likitoci suka bayyana cewa maza bakaken fata musamman ‘yan kasashen nahiyar Afirka sun fi kamuwa da wannan cuta.

Bincike ya nuna cewar wannan cuta na daya daga cikin cututtukan da suke yawan kisan mazaje a duniya.

Alamun wannan cuta sun hada da rashin iya yin fitsari yadda ya kamata,yin fitsari da jini, ciwon kirji da dai sauran su.

Likitoci sun bayyana cewa shan taba,shan giya na kawo cutar sannan akan iya gadon ta daha wurin Iyaye ma cutar.leadershipayau na ruwaito.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button