Allahu Akbar : Gwamnan Zulum Ya Tashi tun Karfe shida na Safe Ya shiga unguwar Da Ruwa sunkayi Ambaliya Yana Tambayar Talakawa Matsalolinsu Gida Gida (Hotuna)
Karfe shida na safe 06:00am ya tashi ya shiga unguwar da ruwa yayi ambaliya yana bi gida gida yana tambayar talakawa matsalolinsu tunkafin wasu su tashi daga bacci…
A zahirin gaskiyar yadda ta bayyana Gwamna Zulum na Borno da gaske yake tafiyar da mulkin al’umma, kuma hakan da yakeyi halayya ce da dama can take cikin zuciyarsa tuntuni…
A tsarin siyasa da yan siyasar wannan zamanin, dole Gwamna Zulum ya tarawa kansa makiya hatta daga cikin wasu masu rike da mukamai a Gwamnatinsa, tunda dai shi ba zaiyi irin halayyar nan ta ko in kula ba, wanda su kuma bara gurbi irinta sukeso, a basu aikin temakawa mutane aki bibiyar yadda sukayi, shi kuwa tunda yana bibiya dole hakan ya janyo masa makiya, sai dai In sha Allah zai cigaba da samun kariya sakamakon addu’o’in alherin da al’umma keyi masa…
Ambaliyar ruwa akayi a wasu bangarori na jihar Borno, amma sai Gwamna Zulum da kansa ya tashi ya shiga Unguwar yana bi gida gida yana tambayar halin da suke ciki kuma ana rubutawa nan take, hatta hanyoyin ruwan da suka lalace duk da idonsa ya ganewa kansa, kuma na tabbatar idan ya bayar da aikin gyarawa zaizo da kansa ya duba…
Ina ma dai irin wannan tsarin na Gwamna Zulum akeyi a duk Nigeria, gaskiya da tuni kasarmu ta cigaba….
Zulum mai kawar da Zulumin Talakawan Borno