Uncategorized

Bidiyo: Bai kamata a riƙa yin shiru kan cin zarafi tsakanin ma’aurata ~ Mawakiya Dija

Shahararriyar mawakiyar nan a Najeriya mai suna Dija ta ce akwai hanyoyi da dama da za a iya kawo ƙarshen matsalar nan ta cin zarafi a gida da ake yawan fuskanta tsakanin mata da maza.

Cikin hirar kai tsaye da ta yi da BBC a shafin Instagram, Aphrodija ta ce ɗaya daga cikin hanyoyin ita ce zuwa wajen masana ko ma’aikatan lafiya domin su ba da shawara kan yadda za a tafiyar da irin wannan matsalar.

Ta ce bai kamata a riƙa yin shiru kan irin wannan matsala ba inda ta ce yawan magana a kan abin na iya kawo maslaha inda ta ce tana ƙoƙarin ganin ta haɗa kai da sauran mawaƙa wajen ganin sun yi magana a kan batun domin wayar da kan jama’a,

“Mata da maza suna fuskantar wannan matsala ta cin zarafi a gida” saboda a cewar ta cin zarafi a gida ya na shafar duka mata da maza.
Ta ce akwai buƙatar a ba da gudummawa a wannan bangaren musamman daga shugabanni.

Tarihin Dija da yadda ta fara waƙa

A cewarta, ita ‘yar asalin Kaduna ce, mahaifiyarta kuma ‘yar Zaria. Mahaifinta kuma ɗan ƙasar Saliyo ne.

“Babana ɗan Saliyo ne kuma da ina ƙarama muna yawan zuwa Saliyo amma a Kaduna na girma” in ji Dija.

Ta kuma yi karatun jami’a a Canada kuma tun daga nan ta fara shiga harkokin waƙa.

Sai dai ta ce ba a fara jin ɗuriyarta ba a harkokin waƙa sai a 2014 da aka haɗa ta da mawaƙi Don Jazzy har suka fara aiki tare da shi.

Ta ce ta soma waƙa ne ta hanyar wani fitaccen mawaƙi Don Jazzy wanda shi ne ya buɗe mata kafar fara waƙa.

“(Fara waƙata) ikon Allah ne, kuma tun ina ƙarama ina sha’awar harkar nishaɗi sannan iyayena suna son waƙoƙi,”

Ta ce a 2016 ne ta fara shiga harkokin waƙa, “ina shiga (gasa), yayana yana bani kuɗi na shiga.”

Dija ta ƙara da cewa tana yawan amfani da kalmomin da ta ke yawan ji ne a cikin waƙoƙinta domin ƙara wa waƙoƙinta armashi,

A cewarta, waƙar da ta fito da ita ita ce ‘AWWW’ kuma ta saki waƙar a 2014 ne.
Ta ƙara da cewa wakar ‘Yaro’ ta fara fitarwa wadda ta rera tare da mawaƙi Ice Prince kuma ta ce har yanzu tana fitar da sabbin waƙoƙi.

Abin da ya sa nake yawan sa kalmomin Hausa a waƙoƙina

Dija ta shaida wa BBC dalilan da suka sa ta ke sa kalmomin Hausa a waƙoƙin da take rerawa.
Ta ce tana alfahari da Hausa saboda “yarenmu ne, kuma idan muna labari da abokaina, wasu lokutan ina ɗaukar wasu kalmomi sannan wasu mawaƙan ma suna sa nasu kalmomin.”
Ta ce wani abin da ke ƙara sa ta yin amfani da kalmomin Hausa shi ne ta nuna inda ta fito sannan kuma ta sa wasu su yi farin ciki.
A cewarta, a lokuta da dama ana faɗa mata cewa waƙoƙin Hausa ba sa kawo kasuwa amma duk da haka a cewarta, ba ta ganin abin a matsayin wata babbar matsala.

Kalubalen da Dija fuskanta a waƙa

A cewar fitacciyar mawaƙiyar, ta fuskanci ƙalubale da dama saboda a matsayinta na mace kuma wadda ta ke da yara, “mata har yau muna fuskantar ƙalubale, mutane na shakku.” Dole sai ka wayar musu da kai.
“Duk abin da za ka yi a duniyar nan, za ka ɗan samu wanda zai ce ba za ka iya ba,” amma ta ce “tun da na samu amincewar iyayena, ai bani da matsala.” in ji Dija.

Nasarorin da ta fuskanta

Dija ta ce a sana’arta ta waƙa samun ƙwarin gwiwa shi ne babbar nasarar da ta samu saboda “aikinmu ba abu ne da aka saba da shi ba, balle ni gani a gidan aure.”
Ta bayyana cewa yadda da kai da kuma sa Allah a gaba zai ƙara ba wa mutum sa’a a harkokinsa.bbchausa ce nayi ruwaito wannan labari.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button