[Bidiyo] Matashin da Yayi Ikirarin sayar Da Kansa Akan Naira ₦20M Yace Rashin Ganin Sarkin Waka Ne
Sannan kuma yace shi ba ɗan Kano bane yazo daga Kaduna ne don ganin Naziru Sarkin Waka da baisamu ganinsa ba har wajen kwanaki biyar sai yasa kansa a Kasuwa zai sayar.
Matashin yace shi daga tudun wadar jahar Kaduna musawa round about taka lafiya road yake kuma ainahi sana’ar tela yake.
Matashin yace shi yana sana’ar dinki tela ne kuma yana taba yin waka domin kuwa ya rerawa sarkin waka wakoki biyu ɗaya wanda yaji labarin sarkin Waka Zai zo Kaduna.
Matashi Aliyu Idris yace ya samu masu bukatar sayensa har kimanin Naira Miliyan goma sha biyar #15M inda ya sanya farashin sa a kan naira Miliyan Ashiri ₦20M.
Ga cikakken bayyani nan a cikin bidiyo kan yadda yake son Sarkin waka sha wulakanci sosai Da Shafin Dokin karfe tv nayi hira da matashin.