Labarai

Ta Faru Ta Kare :Za’a Rataye Gawurtaccen Barawo Evans ~ Datti Assalafy

Babban kotu a jihar Lagos ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya wa gawurtaccen barawo mai garkuwa da mutane wanda ya tara biliyoyin Naira wato Evans
Asalin sunansa Chukwudi Dumee Onuamadike amma yafi shahara da sunan Evans, a tarihin Nigeria ba’a taba samun hatsabibin mai garkuwa da mutane kamarshi ba wanda ya tara biliyoyin Naira.
Jarumin ‘dan sanda DCP Abba Kyari ya shafe shekaru yana neman Evans amma ya gagara kamuwa, Evans yana amfani da manyan nu’urori da suke dakile duk wata hanya da za’a ganoshi ta hanyar tracking, yana amfani da manyan wayoyi wadanda basa aiki da simcard irin namu a Nigeria.
Ta’addancin da Evans ya keyi bai tsaya a Nigeria kadai ba, yana tsallakawa kasashe kamar Jumhuriyar Benin, Kamaru da kuma Ghana, yana da yara da suke aikin garkuwa da mutane a karkashinsa.
Sarkin Yaki DCP Abba Kyari ya hana idonsa bacci ya shirya wa Evans mummunan tarko ta sanadin ‘yar uwar Evans din, Abba Kyari ya samu nasaran kamashi a birnin Lagos a ranar asabar 11-6- 2017, wannan kamun ne yayi sanadin karawa DCP Abba Kyari girma daga mukamin ACP zuwa DCP shi da mataimakinsa da sauran yaransa da suka halarci Operation din duk an musu karin girma
An samu biliyoyin naira a asusun ajiyar kudin Evans, an samu manyan gidaje da ya mallaka a birnin Lagos da wasu jihohi da kasashen waje, banda manyan motoci da sauran kadarori, an samu bindigogi kirar AK47 da dubbannin harsashi da sauran kayan ta’addanci a tare dashi.
‘Dan ta’adda Evans ya dauki manyan lauyoyi har da masu mukamin SAN domin su kubutar dashi, sannan ya dauki nauyin wasu kafofin watsa labarai na sharri suna kokarin bata DCP Abba Kyari a lokacin, amma duk baiyi tasiri ba, bayan shekara uku yau kotu ta zartar masa da hukuncin kisa ta hanyar rataya
Allah Ya tabbatar da halaka a kanshi, Ya kuma kara masa nauyin kasa.
Yaa Allah Ka tsare mana Sarkin Yakin Nigeria DCP  Abba Ka kara masa taimako da nasara Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button