Uncategorized

Uwargida Ta Yiwa Kishiyarta Wanka Da Ruwan Zafi A Kano

Wata uwargida ‘yar shekara 26 a unguwar Zango dake birnin Kano, Zulaihat Nasir, ta jiwa kishiyarta, Nafisa Isa, mumunan rauni bayan yi mata wanka da ruwan zafi.

 Zulaihat Nasir (‘Yar Shekaru 26)

A labarin da Jaridar Daily Trust ta ruwaito, Nafisa da Zulaihat na zaman aure ne gidan Ibrahim Sabo, mazaunin jihar Kano. Rahoton ya bayyana cewa wacce aka watsawa ruwan zafin ta ji raunin kuna a kai da kirji kuma an garzaya da ita asibitin Abdullahi Wase.

Zulaihatu wacce ta aikata wannan laifi ta yi bayani a ofishin ‘yan sanda cewa kishiyarta ce ta fara kulleta cikin daki kuma tayi barazanar banka mata wuta. Ta ce ta yi mata wanka da ruwan zafi ne matsayin ramuwar gayya kan kulleta da barazanar da tayi mata.

Tace: “Mun yi fada da ita ne, amma da na koma dakina na, sai ta kulle kofar ta garkameni ciki tana barazanar banka min wuta cikin dakin.” “Tun karfe 4 na yamma ta ke kulle ni cikin dakin har Magariba da Maigidanmu ya dawo gida.” “Saboda haka na fusata kuma na yanke shawarar daukar fansa ta hanyar zuba mata ruwan zafi.”

Amma yayin da jami’an ‘yan sanda ke yi mata tambayoyi, ta bayyana nadamarta kan abinda ta aikata.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Harina Kiyawa, wanda ya tabbatar da labarin ya ce ya faru ne ranar Lahadi, 31 ga Mayu misalin karfe 11 na safe. Ya ce kwamishanan yan sandan jihar, Habu Sani, ya bada umurnin mayar da lamarinta ofishin sashen CID domin bincike mai zirfi.

Ya kara da cewa idan aka kammala binciken, za a caji duk wanda aka kama da laifi zuwa kotu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button