Dole Masallata su Yi Rajista kafin Yin salla A Najeriya
Dole ne Masallatai da Coci-coci su tanadi kundin yi wa mahalarta ibada rajista kamar yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ta gindaya a sharuddan bude wuraren ibada a kasar.
Shugaban Tsare-Tsaren Kwamitin Shugaban Kasa da ke Yaki da Covid-19, Dr. Sani Aliyu ya bayyana haka a birnin Abuja, yayin da ya gargadi cewa, duk da matakin dage dokar haramcin taruwar a Masallatai da Coci, amma gudanar da ibada a gida ta fi tsaro.
Aliyu ya ce, za a rika amfani da kundin rajistan wajen bibiyar bayanan mahalarta wuraren ibadar, domin akwai yiwuwar yaduwar cutar coronavirus cikin sauki a wuraren ibadar.
Babban jami’in ya bukaci gwamnonin jihohi da su hana duk wurin ibadar da ya ki mutunta ka’idojin da aka gindaya.
Daga cikin sharuddan akwai haramcin taruwar jama’a kafin ko kuma bayan gudanar da ibada da kuma yawan goge-goge da tsaftace Masallatai da Majami’un.
Madogara: Rfihausa