Labarai

Gwamnatin Taraiya ta amince da kashe Naira Biliyan 2 domin sayen shanu a Taraba

Gwamnatin Taraiya ta amince da kashe Naira Biliyan 2 domin sayen shanu a Taraba
Ministar Jinƙai da Rage Raɗaɗin Ibtila’i da Ci gaban Al’umma ta Ƙasa, Sadiya Farouq ta baiyana cewa Majalisar Ƙoli ta ƙasa ta amince da fitar da kuɗi, wuri na gugar wuri har Naira Biliyan 2 domin sayen shanu don bunƙasa noman dabbobi a Jihar Taraba.
Da ta ke tattaunawa da manema labarai a fadar Shugaban Ƙasa a jiya Laraba, Ministar ta baiyana cewa tuni ma’aikatar ta ta aika da ƙunshin bayanan buƙatar ma’aikatar guda biyu.
majiyarmu ta samu wannan labari daga shafin jaridar Daily Nigerian hausa Farouq ta ƙara da cewa ɗaya da ga ciki shi ne na neman sabunta kuɗin da za a kashe wajen sayo shanu a Taraba a karkashin Shirin Tallafin Gaggawa ga jihohin da su ka samu ibtila’in rigingimu da rashin tsaro.
Ministar ta ce ma’aikatar ta samu sahakewar kuɗaɗe da su ka kai naira biliyan biyu da ɗoriya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA