Addini

Sautin Murya : Martani Mai Zafi da Tonon Silli Da Sheikh Bello Yabo Sokoto Yayi Zuwa Ga Maikwano

Advertisment

INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJI’UNN
An samu wani mabarnacin Malami yana cewa ya kamata ‘yan Demokaradiyyah su kama Sheikh Bello Yabo Sokoto su kulleshi a kurkuku kar su sakeshi har abada ya mutu a daure
Innalillahi wa inna ilaiHi raji’uun!
Laifin Sheikh Bello Yabo Sokoto a gurinsa shine fada da miyagun ‘yan Demokaradiyyah masu cutar da Musulunci
Mabarnacin Malamin ya san cewa Sheikh Bello Yabo yana da mata, yana da yara, yana da marayu wadanda duk suke karkashin kulawa da ciyarwansa, amma yake kira a kama Bello Yabo a kulleshi har karshen rayuwarsa, kunga daga nan shikenan iyalan Malam Bello Yabo su lalace, yanzu mai fadin wannan idan ya samu dama ba zai hallaka Malam Bello Yabo ba?
To Alhamdulillah Malam Bello Yabo Sokoto ya masa raddin da ya dace dashi, kuma ya tonawa malamin asiri tonon asirin da ba’a taba masa irinsa ba tunda uwarsa ta tsuguna ta haifeshi, wanda ya kamata Malamin ya rataye kansa saboda abin kunya da ya tafka
Wanda a cikin zaku cewa shi wannan malamin mai kwano  yacewa shehunan malamai yan bidi’ah kamar haka:-
1.Dr Muhammad Sani Umar R/Lemo
2. Dr Engr Bashar Aliyu Umar
3 . Prof Mansur Ibrahim sokoto.
Yaa Allah Ka kare mana Malam Bello Yabo, Allah Ka daukaka darajarsa, Allah Ka bashi nasara akan ‘yan ta’adda na fili da na boye Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum
A cikin wannan Audio zakuji yadda Sheikh Bello Yabo ya bashi amsar cewa wadannan malamai sunfi karfinsa.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button