Uncategorized

Ladubban Daren Farko Domin Sababbin Ma’aurata

   Da farko idan zaka shiga dakin Amaryarka, zaka shiga ne da alwala. Sannan zaka nemi ‘Dan wani abinci mai daraja. Misali kamar Naman Kaza, ko Tsire, da sauransu.

   Idan Kashiga zaka umurceta itama taje tayi alwala sannan kuyi Sallah raka’a biyu Sannankuyi ma Allah godiya abisa cika muku burinku da yayi, Kuyi addu’a abisa kanku da dukkan al’ummar da suka amsa gayyatarku suka halarci wajen daurin aurenku.

       Daga nan sai ka dafa kanta Ko goshinta sannan ka karanta wannan addu’ar kamar haka: ((“ALLAHUMMA INNEE AS’ALUKA KHAIRAHA WA KHAIRA MA JABALTAHA ‘ALAIY – WA A’UZU BIKA MIN SHARRIHA WASHARRI MA JABALTAHA ALAIY (kokuma MAJUBILAT ALAIHA)” (Abu dawud ya ruwaito da Ibnu Maajah da Nisa’I).

MA’ANA: “YA ALLAH ina rokonka alkhairin da yake tare da ita, da kuma alkhairin abinda kaginata akai, Kuma ina neman tsarinka daga sharrinta da kuma sharrin abinda ta ginu akansa” Ita wannan sallar Nafilar da akeyi,tazo ne acikin ayyukan Sahabbai. Kamar irinsu Ibnu Mas’ud (rta). Daga nan kuma sai kuci wannan abin da ka shigo dashi, ku dan sha wani abu mai zaqi haka.

     Amma ba’a so mutum yaci abu mai nauyi sosai a irin wannan lokacin, daga nan kumasai ku kusanci juna, tare da gabatar da ‘yan wasanni da juna kafin kufara gabatar daibadar Aure. Kuma akwai addu’ar da ake karantawa daidai lokacin da za’a fara jima’I ita ce:

“AllahuMMa Jannibnash Shaidani Wa jannibiSh-shaydani ma razaqtana”

     MA’ANA: “Ya Allah ka nisantar da shaidan daga garemu, Kuma ka nisantar da shaidan daga abinda zaka azurtamu dashi”.
 
   Annabi (s.a.w) yace: “Idan aka Qaddara samun ciki awannan saduwar, to shaidan ba zai iya cutar dashi ba har abada” (Bukhary da Muslim suka ruwaito shi) Kabi amaryarka ahankali, Domin kuwa wasu amaren zaka iske sun wuni cikin gajiyar biki, sannan ga kunya
ta lullubeta saboda tunanin wannan lokaci mai daraja. Sannan yawancin angwaye suna kwallafaransu akan cewar wai sai sunyi jima’I adaren farko, wannan ba dole bane.

   Idan kaga alamar ta riga ta gaji, to ka kyaleta. Idan kuma tsoro take ji, (musamman ma idan mai kananan shekaru ce, ko kuma Allah ya tsareta bata ta’ba kusantar namiji ba) Zaka tarar ta gama tsorata, wata ma har tana karkarwa (jikinta yana rawa saboda tsoro) Don haka ka kwantar mata da hankali ta hanyar kalamai masu dadi na soyayya, nasiha, da sauransu.

Haka shari’a ta koyar.

 Ya Allah ka aurar da matasanmu maza da mata ga Ma’aurata nagari Ameen ya hayyu ya kayyum.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button