Addini

Budurwa tayiwa Malamai Wankin Babban Bargo da Zagi Kan Wa’azin Bincike Kafin Aure

Budurwa ta yiwa Malamai kudin goro ta zage su kan wa’azi da suke na a gabatar da bincike kafin aure...

Budurwa tayiwa Malamai Wankin Babban Bargo da Zagi Kan Wa'azin Bincike Kafin Aure
Ta tabbata a yanzu mun shigo wani zamani da ake wasan kura da mutuncin Malamai magada Annabawa, kuma duk sanadin cigaban shafukan sada zumunta da muke ciki, domin mafi akasarin masu raini da maganganu na batanci ga Malamai ba dan sun buya a bayan waya ba baza su iya kallon wadanda suke zagi da ido ba su fadi irin maganganun da suke fada.
A ‘yan kwanakin nan wata lakca ta Sheikh Abdallah Gadon Kaya tana yawo a shafukan sadarwa da yake magana kan idan zaka auri budurwa da ake zargin tana bin maza to a tabbatar da tayi jini na gidan su kafin aure, saboda lalacewar zamani.
Sai dai bayan jin wannan jawabi wata budurwa mai suna Fauziyya Muhammad dake amfani da suna peezy234 a dandalin tiktok ta fito tayi fyadar dan kadanya ga Malamai baki daya, bama Malamai kadai ba, a wani dogon bidiyo da ta wallafa a shafinta:
Sakamakon goge bidiyon da budurwar ta yi, mun samu damar gano bidiyon a Tashar YouTube ta Tsakar Gida.
Kalli bidiyon

Ko da ganin wannan bidiyo sai fa aka yi mata caa da la’anta da martani domin kalmar Malai da tayi baki daya ta hada kowa da kowa dana wannan karnin da kuma na karnin da suka shude, inda ake ganin cewa Annabi Muhammad (SAW) zai iya shiga ciki, domin kuwa shine farkon Malami.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button