Uncategorized

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN! Labari Mai Ban Al’ajabi Da Mamaki Da Firgita Da Darasi A Rayuwar ‘Ya Mace

Sunana Maryam ni “yar garin yola ce zanyi wan nan rubutu ko Allah zaisa akwai matan da suke kokarin bijirewa Allah subi rudun duniya.Nasan Ina daya daga cikin mata kyawawa masu kyau lokacin da nake zamanina amma daga karshe shaidan da kawaye suka rudeni da muguwar shawara yau ga rayuwa yadda na kasance ance dama karshen alewa kasa.

nabijirewa maganar iyayena nabi son zuciyata gashi lokacin duniya tana kaina gani nake babu komi yanzu lokaci yakure dan kafin nazo na nemi tuba Allah yayi musu rasuwa.duk cikarki mace idan bakibi Allah da manzonsa ba iyaye da mijinki to wallahi  za kiyi dana sanin rayuwa.nayi mota nayi gidaje nayi gwalagwale duk wata sutura idan tafito ina daya daga cikin masu siya,

yau babu ko daya “yan uwana sun gujeni saboda lalurar da nake ciki yanzu mijina dana masa butulci na gujeshi yanzu shi yake zuwa da yarana su dubani su siya min magani da kayan bukata na yau da kullum .yau duk mata da mazan da nake mu’a mulla dasu ta banza bana kara jin ko ina suke wacce ta fara koyamin neman mata tun kafin nayi aure yanzu tayi aure ta tuba tunda tazo sau daya taga halin da na shiga bata kara dawowa ba

wanda ita tafi amfanata duk duniya kamar yadda miji yake zaman aure da matarsa.duniya makaranta gashi tun ban mutu ba nafara ganin sakamako,wasiyya ta ga mata kubi Allah da manzonsa kuyiwa iyayenku biyayya ku zauna gidan aure ku hakura da inda Allah ya ajjiyeku itace hanyar tsira dan Allah kuyi min Addu,a  idan nazo mutuwa na samu sassauci gurin Allah.

ALLAH ya shiryar damu bisa tafarki madaidaici

Ameen.

ALLAH YA KYAUTA YA GAFARTA MIKI MASU IRIN WANNAN HALI SU GANE SU DAINA.

Daga Jaridar News world hausa

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA