Uncategorized

Abincin Da Yakamata Mu Yawaita Ci A Wannan Yanayi Na Annoba Domin Samun Kariya

Advertisment

Daga Aliyu El-Idrith Shu’aibu (Dan Autan Media)

Masana ilimin abinci sun bayyana cewa akwai bukatar mutane su rika shan cin nau’in abinci da ‘ya’yan itace domin inganta garkuwar jikinsu.

Masanan sun ce cin wadannan na’ika na abinci zai yi tasiri sosai a jikin mutum ta yadda zai ba shi kariya daga cututtuka irin su cutar korona.

Hajiya Zainab Ujudud Shariff, wata masaniyar abinci da tsarin amfani da shi ta shaida wa Manema Labarai nau’ukan abincin da suka kamata a rika ci domin inganta garkuwar jiki:

Zogale

Cin zogale da koren tattasai da kuli-kuli ko kuma tafasa shi a yi sirace da shi sannan a sha ruwansa. Kazalika za a iya mayar da shi gari sannan a rika sanya shi a cikin shayi ana sha. Binciken kimiyya ya gano cewa zogaye yana gyara garkuwar jiki.

Zobo

Shan zobon ruwan da aka hada da citta da kanimfari ba tare da suga da yawa ba yana gyara garkuwar jiki.

Mangoro

Tana karfafa garkuwar jiki. Don aka yana da matukar amfani a wanke mangoro kafin a sha. Yana da kyau a hada mangoro da goba da kankana wuri guda ta hanyar yanka su sanna a sha su lokaci guda.

Kindirmo (Nono)

Kindirmo musamman wanda aka tatso daga jikin saniya kai tsaye yana ingata garkuwar jiki. Amma babu laifi idan mutum ya yi amfani da kindirmo dan kanti.

Kankana
Kankana ita ma tana da matukar muhimmanci wajen gina garkuwar jiki.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button