ME YASA ZANGO YA YI AMAI YA LASHE? Adam A. Zango ya bi sahun ‘yan Kannywood Wurin Yin rijista Da Hukumar Tace Finafinai Ta jihar Kano
A cikin shekarar da ta gabata ne dai jarumin ya fitar da sanarwar ficewar sa a masana’antar shirya Finafinan Hausa wadda aka fi sani Kannywood.
Jim kadan bayan hukumar ta tilastawa duk wani mai ruwa da tsaki a harkar fim yin rijista da su. A cewar hukumar yin rijistar wani tsari ne da zai basu damar dakile kwararowar bara gurbi a Kannywood.
Jarumai da dama dai cikin su har da Zango sun bijirewa umarnin na hukumar tace Finafinai, inda suka bayyana cewa babu wanda ya isa ya sanya su yin rijista da hukumar domin hakan ba ya cikin kundin doka wanda aka kafa hukumar da shi.
Wasu kuwa na ganin an kirkiro tsarin ne da muzgunawa wadanda su ka yi adawa da gwamnatin jihar Kano.
Daga lokacin ne hukumar ta sanya kafar wando da duk wani jarumi ko mawaki da ya bijirewa tsarin na su.
Ko a shekarar da ta gabata hukumar ta haramtawa Zango yin wasan Sallah a garin Kano, kasancewar bai yi rijista da su ba.
Har ila yau idan ba ku manta ba, a cikin watan Fabrairu da ya gabata hukumar ta sake haramtawa Zango shigowa kallon fim din Mati A Zazzau, inda ta sha alwashin kama jarumin matukar ya shigo Kano kallon fim din.
Ana cikin wannan takun saka ne kwatsam sai aka ga jarumin a yau Talata, ya wallafa takardar da ke nuni da cewa shi ma ya bi umarnin hukumar na yin rijista da su.
Sauran jaruman da ba su yi rijista da hukumar ba, sun hada da: Sani Musa Danja, Yakubu Muhammad, Mustapha Naburaska, Baban Chinedu, Aminu Alan Waka, Aminu Saira, Falalu A. Dorayi, Naziru M. Ahmad, Abdul Amart Mai Kwashewa, Sadik N. Mafia, da sauran su.
Ku kasance da shafukan “Kannywood Exclusive” da Misalin karfe 10pm na daren yau domin jin amsoshin wadannan tambayoyin daga bakin Adam A. Zango.
1.Kana cikin jaruman Kannywood din da suka ce ba za su yi Rijista da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ba. Amma yanzu kuma an ga ka yi mubaya’a. Me yasa?
2. Wannan Rijista na nufin cewa yanzu ka dawo a masana’antar Kannywood. Kasancewar ka sanar da ficewar ka a shekarar da ta gabata?
3. Me za ka ce akan abokan ka (‘yan fim) da kuma yaran ka, wadanda ba su yi rijista ba?