Masu gari: ‘Yar gidan Gwamna Ganduje ta gwangwaje Ado Gwanja da kyautar tsaleliyar mota


“Alhamdulillahi wannan kyautar ta zo mini daga Balaraba, don ku kara tabbatar da cewa mun bi gidan hallaci, ni ke da uwar gaske madalla da kulawa Hajiya Balaraba,” in ji Ado Gwanja.
Wannan kyauta dai ba ta zo da mamaki ba, idan zaku tuna Ado Gwanja yana daya daga cikin manyan mawakan jihar ta Kano da suka yi gwamna Ganduje a zaben da aka gabatar a farkon wannan shekarar a jihar ta Kano. Ko lokacin da aka dinga rade-radin cewa gwamna Ganduje zai sha kasa a lokacin zaben, hakan bai hana mawakin daina wallafa hotunan gwamnan a shafukansa na sada zumunta ba. Hakan ne yasa ake yi masa kallon dan a mutun gwamna Ganduje.


