Kisan da aka yi wa Sarkin Gobir ya nuna tamkar babu gwamnati a Nijeriya – Mawaki Aminu Ala
Shahararren mawaki Aminu Abubakar ladan wanda ake kira alan waka yayi tsokaci akan irin kisan gilla da ankayiwa sarkin Gobir Alh isah Muhammadu bawa wanda shine basarake na farko da ankayiwa kisan gilla tun farko fara ta’addancin yan bindiga, irin kisa na kaskanci da wulakanci.
A cikin zantawar da ankayi mawaki Aminu alan waka da Dclhausa hausa nayi da shi inda yake fadin cewa.
” Irin Kisan da ankayiwa alh isah Muhammadu bawa yana alamtawa duniya cewa kamar babu gwamnati a Najeriya,kamar babu hukuma sai dai wandanda suke wannan aika aika.
Domin kana ganin babu wani sarki da ya fito yayi magana ko wani mai faɗa aji ya fito yayi magana domin mu muna da tsari, duk wanda kaga yana mulki a wajen gobirawa ya kalla, saboda muna da sarakuna sama da ɗari ukku, mune asalin hausawa.
Mu muna da zama lafiya bama tashin hankali, duk inda kaga bahaushe bai tashin hankali“- inji Aminu alan waka.
Ku saurari cikakken bayyani a cikin faifan wannan bidiyo.