Labarai

Babu wani ‘NEXT LEVEL’ ;Da Muka Shiga,Baya Kawai Muke Komawa – Hon. Gudaji Kazaure

Advertisment

Dan Majalisa mai wakiltar karamar hukumar Gwiwa, Roni, Kazaure, ‘Yan Kwashi, a karkashin inuwar jami’iyyar APC, Hon Gudaji Kazaure yace maimakon a shiga Next Level, baya ake komawa.

Hon Kazaure a bayyana haka ne a wani taron manema labarai daya kira don yi tsokaci akan sake baiwa babban gwamnan bankin CBN jan ragamar bankin a shekaru 5 masu zuwa.

Kazaure, ya bayyana rashin jin dadinshi bisa yadda shugaba Buhari ya sake turo Gwamnan Emefele domin kara shugabantar bankin dukda matsal-tsalun tattalin arzikin da aka samu.

”Mun yadda shugaba Buhari mai gaskiya ne tare da yaki da cin hanci da rashawa, kuma munada yakini cewa zamu shiga matakin gaba ”Next Level”da mutane masu gaskiya.”

Advertisment

“Amma abin mamaki, sai gashi ya (Buhari) sake zabar gwamnan ‘CBN’ Emefele a wa’adi na 2.”

“Yakamata kafin a shiga Next Level, a cire duk wasu baragurbi da suke ciki, a kawo wasu sababbi.”

Kazaure dai ya sake cewa har yanzu gwamnatin tana tuhumar Dasuki, Diziani Alisson bayan duk kudin EFCC take zargin su dashi ya fito ne daga CBN.

Hon. Kazaure yayin karin haske gama da batuwa dake cewa akwai wadansu amintattun shugaba Buhari wadanda suka bashi bayanan karya game da abubuwan da suke wakana a kasa.

“Ina mamaki, akwai wadansu mutane da suke biyowa tabayan fage, suna kalamance shugaba Buhari.”

“In har aka cigaba da tafiya a haka, to maimakon a shiga “Next Level” to ba shakka sai dai a koma baya “Back Level”

Sources:jaridar Dimokuraɗiya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button