Labarai
Dan Atiku Abubakar zai Auri Diyar Nuhu Ribadu (Hotuna)
A karshen wannan makon ake sa ran daura auren dan tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar (PDP) da diyar tsohon shugaban EFCC, Nuhu Ribadu (APC).
Manuniya ta ruwaito Aliyu Abubakar Atiku zai angwance da Fatima Ribadu ranar Asabar mai zuwa a Abuja
Jama’a da dama dai sun shiga mamakin auren musamman ganin irin tsattsamar rikici dake akwai tsakanin Atiku da Ribadu.
Ga hotunan su nan harda katin aure.