Hotuna: Kayataccen Gidan Da Aka Kawata Shi Da Zinare Mallakar Marigayi Attajiri Alhaji Mai Deribe A Garin Maiduguri
Marigayi Alhaji Mai Deribe yana daya daga cikin hamshakan masu kudin Afrika da suka mori dukiyarsu kuma har duniya ta dinga sha’awarsu
Deribe ya gina wata gagagrumar fada a Maiduguri wacce magina suka kwashe shekaru 10 suna aikinita kafin su kammala.
Daga cikin manyan mutane a duniya da fadar ta bai wa masauki akwai tsohon shugaban kasar Amurka, Geroge Bush da Olusegun Obasanjo Marigayi Alhaji Mai Deribe babu shakka yana daya daga cikin hamshakan masu kudi a Najeriya a shekarun 1980.
Ya gina gida wanda aka yi shi da ruwan zinari.
Mai Deribe yana cikin attajirai guda 12 a duniya da suka mallaki wani jirgin sama mai kirar Gulfstream G550 a shekarar 1971.
Gidan, wanda ake kira da Gidan Deribe, ya ja hankulan jama’a masu tarin yawa a duniya. Ba abun mamaki bane ganin yadda ya dinga saukar manyan mutane a duniya kamar Yarima Charles da matarsa, marigayiya Gimbiya Diana.
Wadanda suka taba shiga Gidan Deribe akwai tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Sarki Juan Carlos na kasar Spain da tsohon shugaban kasar Amurka, George Bush. Shugaban kasar mulkin soja na wancan lokacin, Janar Ibrahim Babangida, shi ya jagoranci bude fadar zinarin bayan kammala ginin da aka yi.
Daga Mustapha Moh’d Gujba