Kannywood
Ali Nuhu ya ce Chiroki bai tallafa wa kowa a Kannywood ba
Jarumin fina-finan Kannywood Ali Nuhu ya kalubalanci wani mai amfani da shafin Twitter cewa ya bayyana masa mutanen da abokin sana’arsa Bashir Bala, wanda aka fi sani da Chiroki, ya tallafa wa lokacin da tauraruwarsa ke haskawa a fagen wasan kwaikwayo.
Shi dai mutumin, wanda ke amfani da sunan Doctor Kiyawa, ya nuna rashin jin dadinsa ne kan yadda jaruman Kannywood suka yi watsi da Chiroki duk da bukatar taimakon da yake da ita.
A wata hira da gidan talbijin na Arewa 24 ya yi da shi, Chiroki ya yi ikirarin cewa fardusoshi da jaruman Kannywood sun daina sanya shi a cikin fini-finai lamarin da ya sa a yanzu yake sayar da kunun aya.
Please in yi maka tambaya, lokacin da Chiroki yake tashe wa ya yi grooming ko ya taimaka wa?Instead akan kudi menene baya yi wa producers? Let’s be realistic please. https://t.co/ms76P2LJgR
— ali nuhu (@alinuhu) 21 Janairu, 2019
Doctor Kiyawa ya yi zargin cewa mata kan shiga harkar fim cikin shekara guda su yi kudi amma mazan da suka kwashe shekara da shekaru suna harkar ba sa samun komai
“A Kannywood ne za ka ga mace ta shigo film wannan shekarar amma ta fi wadda ya yi shekara 10 yana sana’ar film kudi. Ali Nuhu, kai ne wadda yanzu jama’a suke gani da kima a Kannywood, don Allah ku yi wa [Chiroki] wani abu wadda shi ma ba zai manta da kun yi masa halacci ba.”
Sai dai a jerin sakonnin martanin da Ali Nuhu ya mayar wa masu irin wannan korafi ya kalubalance su da su nuna masa irin taimakon da Chiroki ya bai wa Kannywood.
“Zan yi maka tambaya: lokacin da Chiroki yake tashe wa ya yi taimaka wa? Maimakon haka, a kan kudi mene ne ba ya yi wa fardusoshi? Ya kamata mu san abin da muke yi.”
Ya ce bai kamata a rika yi wa ‘yan Kannywood rashin adalci ba wajen dora alhakin gazawar wani daga cikinsu a kansu.
Jarumin ya ce babu wani da ke Kannywood da zai taimaka wa Chiroki, yana mai cewa “ya kamata ya dawo masana’antar ya sasanta da fardusoshi sannan ya ci gaba da aiki kawai.”
Sources: bbchausa.com
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com