Labarai

ZARGIN RUB-DA-CIKI KAN KUDADE: Zakakurin dan sanda, Abba Kyari ya shiga tsomomuwa

Shahararren dan sandan nan mai kamo ‘yan fashi da kuma barayi da ya yi suna a fadin kasar nan, Abba Kyari, ya shiga tsomomuwa, bayan da wasu kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka zarge shi da yin rub-da-ciki akan milyoyin kudade daga dukiyar da wani da ake zargi ya na garkuwa, ya mutu ya bari.
Wanda ake zargi da aikata fashin dai ‘yan sanda ne suka harbe shi a lokacin da ya ke hanya a cikin mota tare da wasu ‘yan uwan sa a cikin motar.
Sannan kuma tsohon dan sanda ne da ya yi ritaya a mukamin kofur.
A yanzu dai sashen ‘yan sanda mai farautar masu laifukan fashi da garkuwa, wato Intelligence Response Team, su na ta gaganiyar tsame kan su daga cikin wannan tsomomuwa, bayan da wata kungiyar kare hakkin dan Adam da Amnesty International suka rubuta wa hukumar ‘yan sanda kakkausan korafin abin da ta kira yadda su Abba Kyari suka azarta kan su da dukiyar wanda aka harbe a bisa zargin aikata garkuwa da jama’a.
Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta rubuta wa tsohon Sufeto Janar Idris Ibrahim da ya sauka cikin makon da ya gabata takardar korafin daka wa dukiyar mamacin wasoso da suka ce su Abba Kyari sun yi.
Sun kuma rubuta musu yadda aka rika musguna wa iyalan mamacin, tare da karbe dukkan dukiyarv da mamacin ya mutu yac bari ba tare da karbo iznin kwace ta daga kotu ba.
Bugu da kari, a cikin takardar akwai koke na yadda hatta har kudin hayar gidaje da na otal din da mutumin ya mallaka aka yi zargin su Kyari sun rika karba.
Shi dai Collins Ezenwa, yan sanda ne suka harbe shi cikin watan Janairu, 2018, sannan kuma suka rika tatsar dukiyar da ya bari, kamar yadda Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta yi zargi a rubuce.
Kyari dai ya musanta wa PREMIUM TIMES wannan zargi da aka yi masa. A lokacin da wannan jarida ta nemi jin ta bakin sa, ya gargade ta cewa kada ta sake ta buga wannan labari, kuma Ezenwa babban dan garkuwa da mutane ne kafin a kashe shi.
‘yan sandan jihar Imo sun zargi Ezenwa da laifin zama gogarman wata gayyarv masu garkuwa da jama’a. A kan haka ne wata rana cikin Janairu, 2018 suka harbe shi ya mutu, a kan titin Enugu zuwa Owerri.
NHRC ta ce bayan da aka kashe Ezenwa, sai rundunar IRT ta Abba Kyari ta fahinci ya na da dimbin dukiya ta bilyoyin nairori, daga nan sai suka kwace binciken sa daga ‘yan sandan Jihar Imo, suka maida hannun su.
Shi dai mamacin mai suna Ezenwa, ya yi ritaya a daga aikin dan sanda ya na kofur mai daukar albashin naira 47,000 a wata. Ya yi ritaya cikin 2017, ya je Malaysia, bayan wata daya yadawo.
Dawowar sa ke da wuya sai aka ga ya barke ya na ta sayen manyan kadarori, ya na ta bindiga da kudade, tamkar injin buga kudi ya ke da shi accikin gida.
An kuma gano daga baya cewa ya kan rika zuwa Malaysia tun daga 2014, amma ya rika boye wa matar sa da sauran ‘yan uwan sa tafiyar tasa. Ya shiga aikin dan sanda a cikin 2009, an kashe shi ya na da shekara 31.
A Jihohin Kudu maso Gabas ya yi suna da tashe na kankanen lokaci, har aka kiran sa “E-Money.’’
Tun ya na aikinn dan sanda ya rika bindiga da kudi, har kaurin suna yayi wajenn lika kudi a wurin bukukuwa.
Daga cikin kadarorin sa akwai wani kantamemen otal da ka kiyasta kudin sa naira milyan 220,000,000. Ya na da gidajen da aka kiyasta sun kai naira milyan 180.
Wadannnan ne kadarorin da aka gano ya mallaka lokacin da aka rubutawa tsohon Sufeto Janr Idris takarda dangane da batun sa.
Wannan lissafi kuma bai kunshi tsadar bargar motocin sa masu yaq
a ba.
Wani dan sanda mai gabatar da kara mai suna Nosa Uhumwangho, yawa PREMIUM TIMES cewa sunn gano kadarorin Ezenwa a Jihohin Abia da Imo sun kai na bilyoyin nairori.
Ita ma kungiyar Amnesty Inernational ta rubuta wa Sufeto Janar Idris mai ritaya korafinncewa Kyari da tawagarsa sun a kuntata wa matar mamacin. Kuma suna tatsar dukiyar da mijin ta ya m utu ya bari ba tare da kotu ta ba su iznin kwace masa ma gidajen da ya mutu ya bari.
Daya daga cikinnjami’an Hukumar Kare Hakkin Dan Adam mai suna Damian Ugwu, ya shaida wa PREMIUM TIMES su Abba Abba Kyari sama da shakara daya kenan su na karbar kudin hayar gidajen Ezenwa, ba ta tare da neman iznin rike wa gwamnati gidan daga wata kotu.
An kulle matar sa bayan ta haihu tun ba ta kai wata biyu da haihuwa ba. an kashe mijin ta lokacin ta da dauke da ciki dan wata hudu.
Lokacin da aka kama ta, ta yi kwanaki a hannunn su Abba Kyari, inda ya nemi ta kai takardun gidajen mutumin. Ta ce amma ba ta yi haka, ba saboda ta yi zargin dawata manufa aka nemi ta bayar takardun gidaje ko kadarorin sa.
Haka ita da kan ta ta shaida wa PREMIUM TIMES.
’Su Abba ‘yan sandan IRT sun kwace De-Inglish Hotel, mallakar mutumin da wani babban gidan haya da shi ma ‘yan sandan ne ke Kabar kudin.
PREMIUM TIMES dai ta samu sunayen asusun ajiyar da ake zuba kudin idan ‘yan sandan sun karba hayar da suke karba.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button