Sharhin Fina Finai : Sharhin fim Din Sa’eed
Suna: Sa’eed
Tsara labari: Muhammad Sardauna
Furodusa: Sani Shu’aibu
Bada umarni: Muhammad Sardauna
Kamfani: D. Skuare investment Nig. Ltd & Dogon Yaro Movietone
Jarumai: Sadik Sani Sadik, Sulaiman Bosho, Aisha Aliyu Tsamiya, Musa Kalla, Ladidi Tubless, da Balarabe Jaji.
A farkon fim din an nuna Alhaji Buba (Sulaiman Bosho) da yaronsa Kalla suna magana akan wata yarinya da yakeso acikin kauyensu Kadija (Aisha Tsamiya) ‘yar gidan Malam Ladan wadda ita yarinyar ma batasan yana yi ba, yana fadawa Kalla cewar tunda yana da dukiya zai nuna karfin dukiyarsa ko da komai nasa zai kare gurin ganin ya mallaki yarinyar.
An nuna gidansu Kadija suna tsananin soyyaya tare da dan kanin mahaifinta Sa’id (Sadi Sani Sadik) an nuna yanda suke tsananin kaunar junansu kuma mahaifansu an nuna masu zumunci ne kuma suna son kulla alakar auren Kadija da Sa’id amma kuma a gefe guda iyayen su Kadija suna matukar ganin mutuncin Alhaji Buba saboda yanda yake taimakonsu da dukiyarsa domin duk su basu fahimci kudirinsa na kaunar Kadija ne yasa yake yi musu wannan taimakon ba, da Alhaji Buba ya kai wa Kadija kokon barar soyyayarsa yaga abun bazaiyu ba domin hankalin Kadija baya kansa sai ya hada baki da wani abokin Sa’id Alhaji Buba ya tura Sa’id birni kasuwanci domin ya sami damar aure Kadija shi Sa’id bai san dawar garin ba hakan tasa ya fara murna da kuma shirin tafiyarsa birni iyayensa ma suka taya shi murna sosai suka yi masa addu’a da fatan alkairi masoyiyarsa Kadija ce kawai bata son tafiyar Sa’id birni saboda batason rabuwa da shi amma a hakan Sa’id ya lallavata ya bata baki ya kama hanya ya tafi birni neman kudi kamar yanda Alhaji Buba ya tura shi.
Bayan tafiyar Sa’id Alhaji Buba ya sami damar vullowa da Malam Ladan da Malam Sunusi iyeyen su Sa’id maganar aurensa da Kadija dukkansu babu wanda ya bashi goyon baya saboda zumuncin da suke son kullawa tsakanin Kadija da Sa’id ganin haka Alhaji Buba ya saka yaransa cikin dare suka je suka kakkashe Kaf iyayensu Sa’id har iyayensu mata basu tsira ba itama Kadija da kyar ta samu ta tsira ta fice tabar garin ta sauka a gidan wani mutumi ya taimaketa ya riketa. bayan Sa’id yadawo daga birni ya tarar da abunda ya faru ya shiga cikin matsanancin tashin hankali na rashin iyayensa da kuma masoyiyarsa don shi duk a zatonsa ma itama Kadijar ta rasu kuma shi duk baisan Alhaji Buba ne ya kullamasa duk wannan makircin ba, shi kuwa Alhaji Buba tunda abun ya faru ciwo ya dirarar masa ya fara jinya sannan duk dukiyar daya mallaka masifa ta afkamata ta kare shi kuwa Sa’id kasuwanci ya havaka ya zama babban mai arziki har Allah ya hadashi da Kadija a hanya ya dawo da ita gida aka daura musu aure shi kuwa Alhaji Buba asirinsa ya tonu cewar shi ya kashe iyayen su Sa’id sanadin dawowar Kadija hakan tasa Sa’id ya saka hukuma ta kama Alhaji Buba da duk yaransa su Kalla.
Abubuwan Birgewa:
1-Jaruman sun yi kokari gurin isar da sakon.
2- An nuna illar zalunci da son zuciya
3- An nuna muhimmancin karfafa zumunci tsakanin ‘yan uwa.
Kurakurai:
1- sauti da camera basu fita yanda yakamata ba a fim din.
2- Shin garin babu shugabancine? anata maganar hakimi amma ba’a tava nunoshi ba duk da tavargazar da aka yi a garin yaci ace maganar ta je gaban hakimi.
3- shin Alhaji Buba ba shida gida ne wanda yake zaune da iyalansa? duk irin arzikinsa da ake fada amma kullum sai dai a ganshi a waje.
4-akwai gurinda Alhaji Buba yake zuwa da kujera ya zauna a kofar gidansu Kadija har iyayenta suke futowa su ganshi a matsayin Alhaji Buba na maikudi kuma cikakken mutum baikamata ace yana yawo da kujera a hannunsa da kansa ba.
5- A matsayin mahaifiyar Kadija na matar aure bai kamata ace ta dauki filo ta danne wuyan Kalla a kofar gida ba.
6-Akwai gurinda Kadija take futowa zance gurin Alhaji Buba a matsayinta na wadda batasonsa kuma iyayenta basa goyon bayan sonda yake yi mata yaya akayi Kadija ta fito? da kuma izinin wa? ko dama abunda suke fada duk ba haka bane?
7-Lokacin da Kadija tabar gida a gigice kuma kawai mai kallo sai ganta a wani gida mai gidan ya taimaketa kuma ana maganar bama a garin bane ba’a nuna ta yaya akayi ta tsira ba sannan da wana kudin motar tabar garin ita da ta fito cikin dare babu shiri.
8-shin duk su Malam Ladan basu da kowa ne ‘yan uwa ko abokan arziki kuma cikin gari irin wannan a wayi gari an kashe har mutum hudu amma babu wani mataki da aka dauka a hukumance?
9- shin Sa’id ba shida kowa ne daga shi sai aboki yake rayuwa? kuma wacce sana’a yake yi a birni da har ya yi wannan arzikin lokaci daya?
10- Akwai gurin da Sa’id yake haduwa da Kadija akan titi ita da wadda suka taimaka mata bayan ya fidda ran ta mutu daga nan kuma aka gansu a wurin wani shakatawa amma ba tare da wacce ya gansu tare ba shin ita wacce suke taren komawa gida ta yi? idan kuma da
ga baya ne ya kamata ace an nuno su tare da wanda ya taimaki Kadija saboda taimakon da ya yi musu.
Karkarewa:
Labarin fim din ya yi kyau amma akwai abubuwan da akayi yi su a dunkule ya kamata ace an bayyanawa mai kallo su sannan an takaita abubuwa dayawa. Wallahu a’alamu!