Kannywood

Jaruma Ta Sa An Daure Daraktan fim Saboda Naira Dubu 500

– Jarumar dai mai suna Zainab Salmanu kamar yadda muka samu

– Ta ce ta bashi kudin ne bisa yarjejeniyar cewa zai hada mata fim amma sai yaki

Kotun shari’ar musulunci dake a karamar hukumar Fagge da jihar Kano ta maka babban daraktan fina-finan Hausa na masana’antar Kannywood din nan mai suna Mansur Sadiq zuwa gidan yari bisa wasu makudan kudaden da ya cinyewa wata jaruma.

Jarumar dai mai suna Zainab Salmanu kamar yadda muka samu, ta shigar da karar ne a kotun inda take tuhumar daraktan da cinye mata zunzurutun kudi har Naira dubu 500 tun a shekarar 2014.

 Jarumar ta ce ta bashi kudin ne bisa yarjejeniyar cewa zai hada mata fim amma sai yaki ya hada sannan kuma ya cinye kudaden ya hana ta.

Tuni dai kotun ta bayar da umurnin kama daraktan inda kuma ta tura shi gidan yari har ya shafe kwanaki 3 kafin daga bisani a warware matsalar inda aka biya jarumar kudaden ta.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button