Kannywood

Wata Sabuwa ! Harkar Youtube Ba Kasuwanci Ba ce – Alhaji Sheshe

FITACCEN mai shirya finafinan Hausa ɗin nan, Alhaji Sheshe, ya bayyana tura finafinai da waƙoƙi da ‘yan Kannywood ke rige-rigen yi a YouTube matsayin wata harkar kasuwanci da cewa ba ta da wata riba. A cewar sa, “makauniyar kasuwa ce.”

Alhaji Sheshe ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawar su da mujallar Fim dangane da cigaban da aka samu da hanyar sanya finafinai a YouTube bayan durƙushewar Kasuwar Ƙofar Wambai a Kano, da kuma rashin samun damar tura finafinai garuruwa masu nisa da aka riƙa yi saboda yanayin da Nijeriya ta ke ciki.

Babban furodusan ya ce: “A gaskiya, ni ban ɗauki harkar YouTube a matsayin wata harkar kasuwanci ba, domin kuwa idan ka duba harkar, wasu kawai ake nema wa kuɗi, musamman ma dai mu masu fim na Kannywood da mu ka shiga harkar ba tare da tsari ko ilimi ba.

“Don haka sai ya zama wasu kawai mu ke nema wa kuɗi, kawai su na ba mu ɗan abin da bai taka kara ya karya ba.”

Ya ci gaba da cewa, “Harkar YouTube wata irin harkar kasuwanci ce da ba ka san yanayin kuɗin da ka samu ba a wata, sai dai kawai ɗan abin da su ka turo maka.

“Amma dai idan ka ji yadda ake samu, abin sai ya ba ka mamaki.

“Ni na gwada, sai kawai na ga duk abin wasu ake nema wa kuɗi, domin na saka fim ɗin ‘Taƙaddama’ a YouTube. Duk da fim ɗin ya na cikin finafinan da su ka yi kasuwa a lokacin da ya fita, amma abin da na samu na yi mamaki, don ni sai na ji kunyar bayyanawa.

“Kuma na saka waƙar I.G. na ‘yan sanda da na yi, amma shi ma abin da na samu a wata sai na ga bai taka kara ya karya ba, don haka sai na ga wannan ba kasuwanci ba ce, domin za ka zuba kuɗin ka ne ba ka san ko nawa za ka samu ba.

“Yanzu abin da zai ba ka mamaki shi ne wanda ya fi kowa yawan mabiya a YouTube, a Arewa, duk da ba zan faɗi sunan sa ba, to shi ne ya fi kowa kukan babu a cikin mu!

“Kuma idan ka duba gidan talbijin na Arewa24, su na kan YouTube, kuma ana ganin su ne na biyu a yawan mabiya, amma sai da su ka fitar da wata sabuwar manhajar da masu kallon su za su rinƙa kallon su.

“Don haka za ka ga abin duk buge ne kawai!”

Daga ƙarshe, Alhaji Sheshe ya yi kira ga masu sana’ar fim ɗin Hausa da su ƙara bincike wajen samar wa kan su hanyoyin tallata finafinan su, kada su dogara da hanyar YouTube domin, a cewar sa, “a gaskiya wannan ba wata hanyar kasuwanci ba ce mai ɗorewa.”

#fimmagazine

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button