Labarai

Darakta Ya Rataye Kansa A Jihar Kogi Saboda Rashin Biyan Albashi Na Watanni Sha Daya

Wani darakta a jihar Kogi mai suna  Edward Soje ya rataye kan sa a jikin wata bishiya saboda rashin karbar albashi na kusan watanni sha daya.

Daraktan dai ya hallaka kansa ne kwanaki goma bayan matar sa ta haifa masa ‘yan uku a wani asibiti mai zaman kan sa dake Abuja.

Soje ya rataye kansa ne a lokacin da ya ziyarci matar sa a Abuja, inda ya bar mata wasikar ban kwana, yana yi mata nasiha cewar Allah zai kula da ita da jirajiran ta guda uku.

 Daga Sani Twoeffect Yawuri

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button