Uncategorized

Kotu Ta Tura Shugaban Jam’iyar PDP Na Jihar Jigawa Zuwa Gidan Wakafi

Kotu Ta Tura Shugaban Jam’iyar PDP Na Jihar Jigawa  Zuwa Gidan Wakafi

Kotun Majistare Ta Biyu Dake Zaman Ta a Birnin Dutse Jihar Jigawa Ta Tura Shugaban Jamiyyar PDP Na Jiha Alhaji Salisu Mahmuda Da Wasu Tsaffin Makarraban Gwamnatin Jihar Jigawa Su Biyar Zuwa Gidan Yari Har Zuwa Ranar 23 Ga Wata Domin Yanke Hukunci Akan Bukatar Bada Belinsu Kamar Yadda  Lawyoyi Suka Bukata. 

Ana Zargin Alhaji Salisu Mahmud Tare Da Tsaffin Kwamishinoni Biyar Da Jam’ian Kungiyar Shugabannin Ma’aikatan Kananan Hukumomi Ta ALGON Da Aikata Lefuka Hudu,  Wadanda Suka Musanta.

Sauran Wadanda Ake Tsare Dasu Tare Da Shugaban Jamiyyar Ta PDP Sun Hadar Da Tsaffin Kwamishinonin Kananan Hukumomi Salisu Saleh Indirawa Da Nasiru Umar Roni Da Shehu Umar Chamo Da Tsoffin Shugabannin Kananan Hukumomin Gagarawa Mukhtar Ibrahim Gongal Da na  Kirikasamma Abba Mohammed Daguro.

Ana Zargin Sune Da Cin Amanar Gwamnati Wanda Hakan Ya Sabawa Sashe Na 97 Da 312 Da 123 Da Kuma Na 287 Na Dokar  Final Code.

Duk Da Yake Sun Musanta Zarge Zargen Lauyan Mutanen Barista Yakubu Abdullahi Rubah Ya Nemi  Belinsu Tun Da Yake Yansanda Ne Suka Gayyaci Mutanen Kuma Suka Amsa Gayyatar. Amma Alkalin Kotun Mai Sharia Usman Muhammed Lamin Ya Dage Sauraren Karar Zuwa 23 Ga Watan Da Muke Ciki.

©Rariya

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button