Uncategorized

Na Tuba Daga Zina Yaya Iddata? -Dr Jamilu Yusuf Zarewa

Na Tuba Daga  Zina, Yaya Iddata ?

Tambaya:
Assalamu Alaikum warahmatullah Malam ina da tambaya Dan Allah macen da tayi zina kwana nawa ne ISTIBRAI din ta?

Amsa:
To ‘yar’uwa Allah ya haramta zina kuma ya sanyata daga cikin mayan zunubai wadanda şuke jawo narkon azaba. Idan mazinaciya ta tuba, malamai sun yi sabani game da iddarta.

1. Akwai wadanda suka tafi akan cewa za ta yı jini uku, saboda maniyyin ya shiga mahaifa, don haka ya wajaba ayı abin da zai tabbatar da kubutarta, kamar yadda wacce aka sadu da ita da kuskure za ta yi, da kuma wacce aka şaka.

2. Za ta yi jini daya kawai, saboda fadin Annabi S.a.w. “Ba’a saduwa da mai ciki har sai ta haihu, wacce ba ta da ciki kuma sai ta yi haila daya” Kamar yadda Abu-dawud da Ahmad suka rawaito.

Don neman Karin bayani duba Almausu’a Alfikhiyya Alkuwaitiyya 30/341.
Zance na karshe ya fi inganci, saboda kusancinsa da saukin sharia, Saboda babban manufar idda ita ce kubutar Mahaifa kuma tana tabbata da jini daya, sannan iddar matar aure ta banbanta da ta mazinaciya, saboda iddarta ana tsawaitata ne don fatan miji zai yı iya yın kome, hakan kuwa babu shi a iddar zina.

Allah ne mafi Sani.
Dr. jamilu Yusuf ZAREWA
2222016

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button