Uncategorized

An Gano Matsalolin Dake Haifar Da Rashin Samun Haihuwa Ga Namiji

Mujallar haihuwa da yadda ake rashin ta wadda aka wallafa cikin watan Satumba na shekarar 2017 ta bayar da ma’anar Infertility a matsayin wata cuta wadda take tattare da rashin samun shigar juna biyu ko kuma cikin bayan da aka yi wata goma sha biyu ana samun saduwa tsakanin mata da miji. Ita matsalar tana iya kasancewa ta mutum daya ko kuma ta su biyu.

Yadda za a iya kawo dauki danagane da rashin haihuwa, abin anan iya yin shi cikin kasa da shekara daya, wannan kuma ya danganta ne danagane da asibiti, al’amarin saduwa, da kuma tarihin al’amarin haihuwa, shekaru yadda su mutanen suke, da kuma shi binciken da aka yi.
Har ila yau ita mujallar ta bayyana al’amarin (infertility) wato rashin haihuwa tamkar wata cuta ce, wadda take samar da matasalar rashin aikin wani abin daya shafi ita cutar.
An samu wani sabon sunan ne a wani taron da aka yi da kwararru 50 a Geneba, akan al’amarin daya shafi haihuwa kuma Hukumar lafiya ta duniya zata amince da shi.
Sabon sunan ya kalli cewar dukkan mata da miji ko wanne yana da gudunmawar daya bayar dangane da shi al’amarin, bugu da kari kuma ita sanadiyar ta rashin samun cikin an raba ne kashi 50 a mace hakanan ma sauran 50 ga namiji.
Abubuwan da suke samar da rashin haihuwa
A Afrika ta Kudu da Sahara ala’amarin daya ke samar da rashi haihuwa shi ne, ya karkasu abin kuma ya fara ne da Akashi 20 zuwa 46, sai kuma kamar kashi 30 na abubuwan da suke taimakawa wajen rashin samun haihuwa, abin ya dangantane ne ga mace, sai kuma kashi 30 ga namiji, da akwai kuma kashi 30 na su biyun ne, wato mace da namiji. ya yin da kuma sauran kashi 10, ba wata maganar da za a yi dangane da hakan.
A kasar Nijeriya shi ala’amarin wanda ya danganci wancan dalilin ya tsaya ne tsakanin kashi 20 zuwa 25 na wadanda suka yi aure.
Dalilan da suke taka rawa dangane da al’amarin rashin haihuwa abin an raba shi ne gida biyu, da farko abinda ke kawo rashin haihuwar namiji wanda kuma babban al’amari shi ne raguwar yadda ruwan maniyi yake, sai kuma ita nata mace.

Babbar matsalar rashin samun haihuwa ga namiji ita ce yadda ruwan maniyi baya zuba da yawa,da kuma rashi taruwar shi, sai kuma wani al’amari wanda ya shafi tashin inganci ko kuma wata matsala ta shafi motility ko kuma morphology ko kuma dukkansu gaba daya . Su wadannan matsalolin suna iya samar da matsalar rashin samun haihuwa ga namiji abinda ya hada da kasancewa cikin yanayin zafi na wani lokaci mai tsawo musamman ma kasa, ga kuma al’amarin
matsalar wani haske a kimiyyance, sai maganar matsalar data shafi muhalli yadda ake samun gurbacewar shi, ga kuma al’amarin daya shafi shan giya da kuma shan Taba sai kuma wasu sauran al’amuran.
Wani binciken da ba dadeda yin shi ba ya bayyana yanayin yadda kasan namiji ya ke shi ne sanadiyar rashin samun shigar ciki kamar dai yadda aka bayyana, hakanan an san cewaraiki ko kuma amfanin testicular wajen samun damar samar da maniyi wannan kuma ya danganta ne, da irin hali ko kuma yanayin da ake ciki. Amma dai ba a bukatar ta wuce 2 degrees Celsius zuwa 4 degrees Celsius wannan shi ne yanayin jikin mutum, wannan ma shi ne dalilin da yasa shi wannan wurin na scrotal sac aka yi a wajen jiki.
Scrotal hyperthermia wani hali ne ko kuma in ce yanayi wanda da ake samun ruwan maniyi wanda baya da inganci, wanda kuma yana da damgantaka da rashin samun haihuwa ta namiji. tabbatar da yanayi mai kyau tsakanin jiki da kuma sactoral sac abin yana da amafani saboda samar da ruwan maniyi mai inganci.
Irin ci gaban kimiyya da kuma fasaha na zamani, shi aikata wani abin kirki ga ala’amarin daya shafi samun haihuwa, saboda kuwa akwai babbar natsalar da ta shafi sctoral sac, saboda idann aka kalli amfani
laptops wadda ake dorawa kan cinya, sai kuma EMF daga wayoyi wadanda aka ajiye su kusa da scrotum, ga kuma al’amarin tuka mota na lokaci mai tsawo, sai kuma al’amarin motocin da ake yin wasa, da yadda wurin zaman mota yake yin zafi sai kuma sai kayayyaki wadanda suka matse jiki da dai sauransu.
Abubuwan da suka kawo canzawar yanayin da sctoral wanda wani wuri ne wanda ake yin shi maniyi.

Na’urar da ake yawan dora ta kan cinya ‘Laptop’
Na’urar komfuta ta Laptop wadda mafi akasari ana dora tane akan cinya ko kuma bisa teburi, wata na’ura ce wadda ita ma takan samar da zafi, wanda kuma ake iya shafar da wani irin zafi wanda shiga ciki . Na’urar Laptop komfuta wadda ake yin aiki da ita,
musamman ma idan tana a wani wurin da zata fi cutarwa, inda kai tsaye ne shi zafin zai shiga cikin sctoral sac. Wannan kuma ya danganta ne akan yadda aka zauna a lokacin amma dai kuma ya kamata a lura sosai a..
An gano cewar yadda ake dora na’urar komfuta laptop akan cinyoyi an gano cewar wannan ne yake taka muhimmiyar rawa wajen karuwar yanayin scrotum ya karu da kimanin degrees 5 Fahrenheit, ko kuma karuwar ku san ( ko kuma kamar 2.7 degrees Celsius). Hakanan kuma an gane cewar yawan taruwar maniyi da kuma yadda yake abin yana yin kasa da kashi 40 , wannan kuma sai idan yanayin rana na scrotal ya yi sama da 1 zuwa 2 degrees Fahrenheit (ko kuma 1 degree Celsius).

Samun matsala saboda wayoyin da ake amfani dasu
Yadda wasu sakonni suke shigowa da kuma irin zafin da waya take fitarwa, shi ma yana iya samar da matsala ba wai kawai ga jiki ba, amma akbin yana shafar abubuwan da suke bada gudunmawa wajen al’amarin samun ciki. Shi sinadarin yana da matukar muhimmaci ga dukkan al’amuran samar da ruwan maniyi. Hakan kuma yana taimakawa wajen yadda shi maniyin zai ya kasancewa mai inganci. Hakanan ma akwai karuwar sosai ta banagaren yawan mizani na
mitochondrial ROS production da kuma shi mizanin 8- OHdG (Reactibe odygen species da kuma wai sinadari na free radicals wanda shi ma zai iya cutar da kwayoyin halitta na gado wadanda aka fi sani da suna DNAda kuma wasu sinadarai na gado, an dai gane cewar su wasu sinadarai wadanda a kimiyyance suna fitowa daga wayoyi RF-EMW, suna iya kara shim s wani sinadari ne wanda yake fitowa daga waya, hakan zai iya shafar, abinda daga karshe na iya zama sanadiyar raguwar maniyi da kuma ingancin shi. Bincike ya nuna cewar ga masu amfani da babbar waya al’amarin zai iya shafar yawan ruwan maniyi ya ragu da kashi 30 fiye da maza wadanda basu amfani da waya.
Saboda haka shi al’amarin amfani da waya abin ana iya shawo kan shi ta hanyar yadda yake rage karfin melatonic a cikin jiki, wannan kuma zai sa shi ruwan maniyin ya samu matsala. Matsalar da way take iya samarwa ba wani abin da za ayi was da shi bane. Saboda illar da hakan zata iya samarwa a gaba.

Wannan ne ma dalilin da yasa yawancin wayoyin da ake sayarwa ake bayar da earpiece wanda ake sawa a kunnuwa.
Zafin gefen motocin wasanni
Zafi daga injin gaba da kuma gefe kokuma wurin da ake zama cikin mota ( musamman ma motocin wasanni saboda suna kusa da injin gaba), suna suba samnar da matsala ga yanayin sctoral, saboda a wannan lokacin suna daidai wurin da abin zai shafe su.
Kwararrun masu tuka motocin wasnni ko kuma direbobi wadanda abin ya kasance masu sana’a, sai kuma wadanda kusan kullun sai sun yi tafiya mai nisa, irin su ba wani abin mamaki bane idan sun samu yanayin sctoral sac nasu ya karu sabida zafin da yake fukantarsu kai tsaye. Ana iya samu rashin ingantaccen maniyi wanda bai iya daukar wani lokacin da za a samu juna biyu. Babbar matsalar ma it ace daukar awoyi masu yawa ana tuki da kuma fasinjoji wadanda suke zama, nan abin yana iya samar da matsala, idan aka yi la’akari da lokacin da aka dauka ana yin su al’amuran.

Sa matsattsun kaya
Duk da yake matsalar da za a iya fuskanta wajen bangaren sa kayan da suke
matse jiki, kamar irin wandunan da masu damben Turawa suke sawa, ko shakka babu abin yana taimakawa wajen ga yadda za a samu yawan ruwan maniyi. Saboda ire- iren wadannan kaya wani lokaci tafiya ma ana iya samun matsalar yin ta, ga shi kuma iska bai iya shiga ciki sosai. Wanan kuma shi zai sa su abubuwan da suke taimakawa wajen alamarin samar da juna biyu daga na miji ko kuma mace su yi zafi. S hi yasa ma zaben kayan da za a sa wannan tana taimakawa wajen daidaituwar al’amura.
Wanka da ruwan zafi
Yin wannan wankan sa kuma sauna sabo shakatawa hakan yana sa mutum ya dan samu armashi, amma hakan ma abin yana iya shafar ingancin maniyi. Cikakken wanka wanda ake shigar da jikin cikin ruwan zafi da kuma mai dumi dumi Jacuzzi ko kuma wurin wanka whirlpool a yanayin da ya wuce 36.9°C zuwa mintuna 30 ko kuma fiye da hakan duk mako, a tsawon wata uku ko kuma fiye da hakan, wannan yana iya sanadiyar kamuwa da wet hyperthermia, wadda kuma tana iya shafar maniyai saboda ba zai samu inganci ba. Masu mu’amala da wannan zasu rika jin zafi amma kuma wanda yake da damshi-damshi, amma kuma wuwraren wanka na zamani suke samar da zafi wanda yake shi busasshe ne da kuma gefe wanda yake da dan dumi-dumi.

Bincike ya nuna cewar banyan an kammala shi wankan na sauna ciin minti goma kuma yanayin jiki zai iya canzawa, wanann ma yana iya shafar kwayoyin halitta na namiji, wannn lokacin kuma yanayin zai iya canzawa abin kuma ya danganta ne daga 80 zuwa 90°C, amma kuma abin ya kan dan bambanta wannan kuma ya danganta ne da lokacin da aka dauka ana yin wankan. Amfani da sauna ta yin wanka abin yana kawo matsala wanda za a samu kwayoyin halitta wadanda basu da inganci. Lokutta da yawa ana samar da Tawul wanda yake da kankara da kuma wani stem saboda adan wartsake.
Kusantar zafi ta hanyar sana’a ko kuma wurin zama
Wani babban al’amari wanda shi ma ba kashin yadawa saboda yana taimakawa wajen samar da gajiya wadda kuam za a rika jin zafi, ga maza wani zafi ne saboda yadda wuraren da ake dangane da yadda shi yanayin wurin yake. Wato inda mutum yake zama ko kuma yin aiki. Ayyukan ko kuma sana’oin da mutane suke yi, abin ya shafi wani dogon lokacin da ake dauka anyin aikin,a kuma samu haduwa da zafi. Masu walda sai kuma yadda suke fuskanta abubuwa masu guba da kuma wuta lokacin da suke yin waldar. Binciken daya shafi wadannan ma’aikatan abin ya nuna a fili ta yadda da kuma dalilan da suka sa ake samu kwayoyin halitta wadanda basu da inganci.

Wadanda suke yin aiki kai tsaye da ta hanyar fuskantar yanayi mai tsananin zafi , kmar ma’aikatan gidan Biredi da kuma wadanda suke kulawa dadakin da ake yin gashi, suna daukar loakci kafin a kai ga samun juna biyu. Wannan kuma ya nuna a fili fuskantar zafi saboda yanayin aiki, abin yana iya shafar maganar samun juna biyu. Mazan da suke yin ayyuka kusa dainda yake da zafi mai yawa kamar kusa da karshen submarine (wurin da motor take) ko shakka babu suna iya fuskantar matsalolin samun haihuwa.

Rahoto daga leadershipayau.ng

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA