Uncategorized
Fatawar Rabon Gado (98) -Dr Jamilu Yusuf Zarewa
Advertisment
Fatawar Rabon Gado (98)
Tambaya
Assalamu alaikum,Allah ya qara wa Dr imani da iklasi,Dr tambaya ce muke da ita,mutum ne ya rasu bai taba aure ba ,sai yan uwa, wadda suke uwa daya uba daya su biyu mace da namiji, sai kuma wadda suke uba daya suma maza biyu da mata biyar, amma iyayen su sun rasu, to yaya za’a raba wannan gadon,shin iya wadda suke daki dayane suke da gadonsa ko sauran ma wadda uba ya hadasu suma suna da gadon? Nagode
Amsa
Wa alaiku assalam, shakikansa, wadanda suke uwa daya, uba daya, su ne kawai za su ci gado a nan, duk namiji ya dau rabon Mata biyu
Allah ne mafi sani
Amsawa
DR JAMILU YUSUF ZAREWA 7/2/2017
05/01/2017
ku kasance da sadeeqmedia ako yaushe domin yada addinin musulunci
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com