Uncategorized

NAMAN DOKI HALAL NE?|DR.JAMILU YUSUF ZAREWA

Advertisment

NAMAN DOKI HALAL NE

Tambaya :
Assalamu Alaikum dan Allah tambayar ita ce shin akwai wani hadith ko Aya wacce ta nuna cewa cin naman [doki] haramun ne?

Amsa :
To Dan’uwa babu wata aya baro-baro ko wani hadisi wanda ya haramta cin naman doki, kuma mafi yawan malamai sun tafi akan hallacin cin naman doki, saboda hadisin Asma’u ‘yar Abubakar, inda take cewa :
“Mun soke wani doki a zamanin annabi s.a.w sai muka cinye shi”
Bukhari : 5191
Saidai Ibnu Abbas da Imamu Malik sun tafi akan haramcinsa, saboda Allah ya fada a cikin suratu Annahl aya ta : 8 cewa ya halicci doki ne don a hau, a kuma yi ado, wannan sai yake nuna ba za’a ci ba.
Zance mafi inganci shi ne hallacin cin naman doki, saboda hadisin da ya gabata, sannan ayar da Imamu Malik ya kafa hujja da ita ba ta fito baro-baro ta hana cin doki ba, domin kasancewar an ce ana hawanta ko ana ado da ita, ba ya hana a ci .
Don neman karin bayani duba tafsiri Kurdubi 1068
Allah ne mafi sani
               AmsawaDr.jamilu zarewa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button