Uncategorized
MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BIN TA AZUMI !|DR JAMILU YUSUF ZAREWA
Advertisment
MAHAIFIYATA TA RASU, ANA BIN TA AZUMI !
Tambaya :
Aslm mlm dan Allah ina da tambaya : tun kafin a kama azumi uwata ba ta da lafiya har akayi sallah, rana ta 16 ga watan karamar sallah Allah yayi mata rasuwa, shin za mu ranka mata azumi ko ba sai mun ranka ba ? Allah ya saka da hairi.

Amsa :
To malam mutukar rashin lafiyar ta zarce mata, har zuwa lokacin mutuwarta, to ba za ku rama mata ba, tunda ba sakaci ta yi ba, saboda fadin Allah madaukaki :
To malam mutukar rashin lafiyar ta zarce mata, har zuwa lokacin mutuwarta, to ba za ku rama mata ba, tunda ba sakaci ta yi ba, saboda fadin Allah madaukaki :
“Kuma duk wanda yake mara lafiya ko matafiyi to sai ya rama a kwanaki na daban” Bakara aya ta : 185, wato bayan Ramadahana,
idan mara lafiya ya samu sauki, ko matafiyi ya dawo , Ka ga wanda bai samu sauki ba har ya mutu, zai zama bai kai lokacin da zai rama ba, don haka sai ya saraya akan shi . .
Amma idan ta samu damar ramawa, ta yi sakaci ba ta rama ba har ta mutu, to sai makusancinta ya rama mata, saboda fadin Annabi s.a.w.
: “Duk wanda ya mutu akwai azumi akansa, to sai makusancinsa ya rama masa” .
kamar yadda Bukhari ya rawaito shi a hadisi mai lamba ta : 1851. Duba Fataawa nuru aladdarb lamba ta : 247.
Allah ne mafi sani
Amsawa
Dr.jamilu zarewa
Dr.jamilu zarewa
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com