Uncategorized

FATAWAR RABON GADO (54)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

FATAWAR RABON GADO (54)
Tambaya:
Assalamu alaikum, malam wata matsala ce ta taso mun Miji na ne ya rasu sai akace za’ayi rabon gado, ‘ya daya muka haifa,sai ni matar shi,sai kanin shi  da suke uwa1 uba1,sai yan’uwan shi da suke uba 1,sai mahaifiyar shi wanda bata musulunci, mahaifinshi ya rasu to don Allah yaya rabon yake.
Amsa:
To ‘yar’uwa ina rokon Allah ya yi masa rahama, zaa raba dukiyar da ya bari gida takwas, a bawa ‘yarsa kashi hudu , a ba ki kashi daya,  dan’uwansa da suke uwa 1uba1 a ba shi ragowar, mahaifiyarsa ba za’a ba ta komai ba tun da ba ta musulunta ba, haka nan yan’uwansa da suke uba 1  ba zaa ba su komai ba tun da akwai kanin shi da suke uwa1 uba 1.
Allah ne mafi sani.
Amsawa: Dr jamilu zarewa.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button