Uncategorized
ZAN IYA AURAN WANDA YAKE DAUKE DA KWAYAR SIKILA ?
*ZAN IYA AURAN WANDA YAKE DAUKE DA KWAYAR SIKILA ?*
*Tambaya ?*
Assalamu Alaykum, don Allah ya halatta ya hukuncin auran mace da genotype dinku daya da ita, AS AS, ya halatta; sannan yana da fa’ida ko babu? Don Allah a tambaya min malamai, na gode.
*Amsa:*
Wa alaikum assalam,Yana daga cikin ka’idojin sharia tunkude cuta gwargwadon iko.
Ilimin likitanci na zamani ya tabbatar da cewa: idan AS da AS suka hadu za su iya haifar Sikila (1) a cikin duk yara hudu da za su Haifa.
A mafi yawan lokuta musamman a kasashen da talauci ya yi musu katuutu, Sikila yana rayuwa ne cikin wahala, kuma iyayansa ma a wahalce, Saboda raunin jininsu Wanda yake haddasa musu ciwon wasu daga cikin gabobinsu.
Zai yi kyau ma’aurata su yi gwaji kafin aure, in har dukkansu suna dauke da kwayar Sikila (AS) su hakura da yin aure tare, tun da za su haifi yaron da zai rayu a wahale, da rashin Walwala gashi kuma addinin musulunci ya yi nufin sauki da jin dadi ga al’uma.
Dukkan wani abu ba ya faruwa sai da kaddara, saidai riko da sababi abu ne da sharia ta tabbatar, kuma ayoyi da yawa suka yi bayaninsa.
Wanda yake (AS) idan ya auri (AA) za su haifi ‘ya’ya lafiyayyu da iznin Allah, wannan sai ya nuna abin yana da yalwa.
Allah ne mafi Sani
12/10/2016
Amsawa:
*DR. JAMILU ZAREWA*
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com