Uncategorized

HUKUNCIN YIN DILKA|DR JAMILU YUSUF ZAREWA

HUKUNCIN YIN DILKA Tambaya : Mace taba da jikinta ga mata yan’uwanta don ayi mata wanka saboda kwalliya ko irin dilka da halawa din nan wai haramunne? Ko da ta rufe mamanta da mazaunanta? In haramunne kenan daga ina zuwa ina ne tsiraicin mace da bai kamata yar’uwarta mace ta gani ba? Jazakallahu khairaljazaaa. Amsa : To ‘yar’uwa malamai sun yi sabani game da tsaraicin mace ga ‘yar’uwarta musulma, akwai wadanda suka tafi akan cewa : bai halatta ‘yar’uwarta mace ta ga wani abu a jikinta ba, sai abin da ya saba bayyana a tsakanin mata, idan suna zaune isu-isu, kamar kafa da hannu da fuska da wuya da makamacin haka. Saidai abin da mafi yawan malaman fiqhu suka tafi akai shi ne : al’aurar mace ga ‘yar’uwarta musulma tana farawa ne daga cibiya zuwa guiwa, kamar yadda al’aurar maza take a tsakaninsu. Don haka bai hallata ta bari wata mace ta kalli sama da wannan wurin da aka iyakance ba, amma idan kafira ce matar to malamai sun yi bayani cewa ba za ta kalli wani abu ba, sai abin da ya saba bayyana, don haka sai a kula lokacin da za’a je dilka wajan wacce ba musulma ba, don kada garin neman gira a rasa ido . Allah ne maf sani BY
DR.JAMILU YUSUF
POST :
Abubakar Rabiu Yari Sokoto,sokoto state
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button