Uncategorized
FATAWAR RABON GADO (68)|DR JAMILU YUSUF ZAREWA
*FATAWAR RABON GADO (68)*
*Tambaya:*
Assalamu alaikum tambaya mutum ne ya mutu yabar mace da yan’uwansa shakikai ba yara kuma mahaifansa sun mutu to Meye kason matar tasa?
*Amsa:*
Wa alaikum assalam, za’a raba abin da ya bari gida:4, a bawa matarsa kashi daya, ragowar ukun sai a bawa ‘yan’uwansa shakikai.
Allah ne mafi sani
20/10/2016
Amsawa:
*Dr Jamilu Zarewa.*
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com