Uncategorized

BA’A GAYYACE NI BA BIKIN SARKIN MUSULMI – Bafarawa

BA’A GAYYACE NI BA BIKIN SARKIN MUSULMI – Bafarawa
Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Alh. Attahiru Dalhatu Bafarawa yace bai je wajen bukukuwan cikar Sarkin Musulmi Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar na III shekaru goma saman karagar mulki domin ba’a gayyace shi ba.
Jami’in Yada Labarai na Jam’iyyar PDP a jahar Sokoto Yusuf Dingyadi ne yayi magana adadin Bafarawa “Har zuwa ranar bikin babu wani katin gayyata daga gwamnati ko kuma kashin kai da aka aikowa Bafarawa domin ya halarci taron. Bafarawa ya baro Abuja tun mako daya kamin bikin da tunanin cewa za’a kira shi domin gudanar aikinsa a matsayin Garkuwan Sokoto”
Ya zargi wadanda suka shirya bikin na kin girmama Bafarawa da kowace dama, wanda hakan ne ya sanya shi kuwa bai halarci bikin ba domin kaucewa tozarta da hakan kan iya janyo wa.
Dingyadi ya kara da cewa duk da haka, Bafarawa zai cigaba da kasancewa mai son cigaban Sarkin Musulmi da kuma Daular Usumaniyya.
Sakkwato Birnin Shehu
7th November, 2016
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button