Kannywood

Maza ne Da Wahala Samu Amma ko Yanzu Na Samu Miji zanyi Auren Irin Mu Inji Rashida Abdullahi mai Sa’a

Advertisment

Fitacciyar tsohuwar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana’antar Kannywood kuma ‘yar siyasa mai suna Rashida Adamu ta bayyana cewa suna matukar shan wahala yanzu wajen samun mazajen aure.

Jarumar dai ta bayyana hakan ne a ‘yan kwanakin nan kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu inda kuma aka ruwaito cewa ta bayyana cewa a duk lokacin da ta samu mijin aure, to fa da gudu zata aure shi.


NAIJ.com dai ta samu cewa majiyar tamu ta ruwaito jarumar na cewa: “Samun Mazan Ne Da Wahala, Amma Ko Yanzu Na Samu Miji Da Gudu Zan Yi Aure”.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jarumar tuni ta dauke kafar ta daga fitowa a matsayin jaruma a cikin fina-finai sannan kuma ta tsunduma cikin harkokin siyasa inda daga baya ma har ta samu mukamin mai bayar da shawara ga Gwamnan jihar ta Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button