Labarai

Garin da maza basa auren macen da ta wuce sakandare a jihar Kano

Na yi imani cewa duk yayin da lokacin aurena ya yi Allah zai kawo min miji.

Tun da dadewa aka bayyana ilimin ’ya’ya mata a matsayin wani bangare na ci gaban al’umma wanda yake samun tallafi daga kungiyoyi masu zaman kansu a ciki da wajen kasar nan don karfafa gwiwar al’umma a kan lamarin.

Sai dai duk da irin wannan tagomashi, ilimin matan har yanzu yana fuskantar kalubale musamman a Arewacin kasar nan inda ake alakanta hakan da addini da al’ada da sauransu.

A yanzu haka al’ummar garin Jemagu a Karamar Hukumar Warawa a Jihar Kano, yara mata ba su yin karatun da ya wuce sakandare saboda idan har suka yi karatu mai zurfi sukan fuskanci matsala wajen yin aure domin mazan garin ba sa auren macen da ta yi karatu fiye da sakandare.

Aminiya ta ruwaito cewa ,Mazan garin Jemagu sun yi imanin cewa matan da suka yi karatun gaba da sakandare idonsu na budewa yadda maza ba su iya juya su ba.

Mutanen garin sun bayyana cewa ilimin ’ya’ya mata yana farawa ya kare a makarantar firamare da sakandare.

Babangida Adamu yana daya daga cikin mazan garin Jemagu da ya ce babu shi ba auren wadda ta yi Boko
Babangida Adamu yana daya daga cikin mazan garin Jemagu da ya ce babu shi ba auren wadda ta yi Boko

Babangida Adamu yana daya daga cikin mazan garin Jemagu, wanda ya yi imanin cewa bai kamata mutum ya auri macen da ta yi karatu fiye da sakandare ba.

 

Ya kara da cewa matan da suka yi karatu mai zurfi ba su son auren mazan da ba su da ilimin boko.

“Maganar gaskiya duk macen da ta yi karatu mai zurfi ba ta son auren mutumin da ba ya da ilimi mai zurfi.

“Ni ba zan auri macen da ke da digiri ba bayan ni ba ni da digiri. Hakan ya sa maza da yawa ba su son auren macen da ta yi zurfi a karatu,” in ji shi.

Sai dai Khadija Muhammad Jemagu mai shekara 25 da haihuwa wacce a kwanan nan ta haɗa karatun difloma a bangaren kasuwanci a Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Kano, ta ce ta yanke shawarar taimaka wa kungiyoyi masu zaman kansu don bunkasa ilimin ’ya’ya mata a yankinsu.

Ta bayyana cewa akwai bukatar a wayar wa iyaye kai a kan muhimmanci ilimin ’ya’ya mata.

A cewar Khadija mutane da yawa sun faɗa mata cewa tunda ta zaɓi ilimin boko zai yi wahala wani namiji ya zo kusa da ita, domin mazan suna ɗaukar cewa ta fi su wayewa saboda ba su yi karatu mai zurfi ba.

Karanta karin bayyani a AminiyaMr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button